Labarai

Ƙaramar Hukumar Bichi ta cilla yawan ƙuri’un Gawuna sama

Ƙaramar Hukumar Bichi ta cilla yawan ƙuri’un Gawuna sama

Daga WAKILINMU Ƙuri'ar yankin Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano, ta taimaka wajen cilla yawan ƙuri'un ɗan takarar Gwamna na APC sama wanda hakan ya sake bai wa ɗan takarar damar shige gaban takwararansa na jam'iyyar NNPP. Da fari Abba Kabiru Yusuf ne ya kasance kan gaba a yawan ƙuri'u, kafin daga bisani lamarin ya juya kan Nasir Gawuna na APC. Bayan wani lokaci NNPP ta sake shigewa gaba har zuwa lokacin da aka bayyana sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Bichi, a cibiyar tattara sakamakon zaɓen. Daga nan ne Nasir Gawuna na APC ya sake tsere wa Abba a yawan ƙuri'u…
Read More
Yanzu-yanzu: INEC ta ce za a yi ‘inconclusive’ a Kano

Yanzu-yanzu: INEC ta ce za a yi ‘inconclusive’ a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana zaɓen ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Takai a majalisar dokokin jihar Kano a matsayin ‘inconclusive’. Jami’in hukumar, Farfesa Usman Ibrahim na Jami’ar Bayero, Kano, ne ya bayyana hakan a ofishin INEC da ke Takai a ranar Lahadi, 19 ga Maris, 2023. “Duk da cewa ɗan takarar jam’iyyar APC, Musa Ali ya samu ƙuri’u 24,573 yayin da ɗan takarar jam’iyyar New NNPP ya samu ƙuri’u 23,569, amma har yanzu ba mu da wani zaɓi da ya wuce mu bayyana zaɓen a matsayin ‘inconclusive’. “Wannan ya faru…
Read More
Raɗɗa ya zama Gwamnan Katsina mai jiran gado

Raɗɗa ya zama Gwamnan Katsina mai jiran gado

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe, INEC, ta ayyana ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar APC a Jihar Katsina, Dr. Dikko Radda, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar a zaɓen da ya gudana ranar Asabar. Raɗɗa ya kai bantensa a zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri'u 859,892 wanda hakan ya ba shi damar doke abokin hamayyarsa na PDP, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke, wanda ya samu ƙuri'u 486,620. Baturen zaɓen kuma Mataimakin Shugaban Jami'ar Tarayya da ke Gusau, Farfesa Mu’azu Gusau ne ya bayyana Raɗɗa a matsayin gwamnan Katsina mai jiran gado.
Read More
Inuwa Yahaya ya lashe zaɓen Gwamna a Gombe

Inuwa Yahaya ya lashe zaɓen Gwamna a Gombe

Daga BASHIR ISAH Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya sake lashe zaɓe a matsayin Gwamnan Jihar Gombe ƙarƙashin Jam'iyyar APC a zaɓen gwamnoni na 2023. Ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu mafi yawan ƙiri'u a ƙananan hukumomi 11 da jihar ke da su. A ranar Lahadi Baturiyar zaɓe a jihar, Farfesa Maimuna Waziri ta ayyana Inuwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri'u 342, 821. Wannan shi ne karo na biyu da Inuwa ke zama gwamna a jihar ta Gombe.
Read More
Ɗan takarar gwamnan APC a Sakkwato na gab da lashe zaɓe

Ɗan takarar gwamnan APC a Sakkwato na gab da lashe zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA Ɗan takarar gwamna a Jam’iyyar APC, Ahmed Aliyu na gab da samun nasara bayan ya lashe ƙananan hukumomi 16 cikin 20 da aka ayyana kawo yanzu. Sakkwato tana da ƙananan hukumomi 23. Aliyu ne ke jagorantar ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Sa’idu Umar Ubandoma da ƙuri’u 41,585. A sakamakon zaven, ɗan takarar APC ya samu ƙuri’u 352,606 yayin da Ubandoma ya samu ƙuri’u 311,021. Ana ci gaba da jiran sakamakon sauran ƙananan hukumomi uku da suka rage.
Read More
Buni ya lashe zaɓen gwamnan jihar Yobe

Buni ya lashe zaɓen gwamnan jihar Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Gwamna Mai Mala Buni na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamna a jihar Yobe. Kwamishinan Hukumar INEC na jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Abdullahi shi ne ya sanar da hakan a cibiyar tattara sakamakon zaɓen dake Damaturu, da daren nan. Ya ce Gwamna Buni na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 317,113, fiye da na abokin takararsa daga jam'iyyar PDP, Hon. Shariff Abdullahi, mai adadin ƙuri'u 104,259, wanda hakan ya tabbatar da Buni a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen.
Read More
Abdulrazaq ya sake lashe zaɓen gwamnan Kwara

Abdulrazaq ya sake lashe zaɓen gwamnan Kwara

Daga SANI AHMAD GIWA Hukumar Zaɓe a Jihar Kwara ta sanar da AbdulRahman AbdulRazaq a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da ya gudana a ranar Asabar. Hakan na nufin ya samu wa'adin mulki na biyu kenan. AbdulRazaq na Jam'iyyar APC ya doke Alhaji Shuaib Yaman Abdullahi na Jami'yyar PDP da kuma Alhaji Hakeem Oladimeji Lawal na SDP. Babbar jami'in da ke lura da zaɓen wato Farfesa Isaac Itodo ya bayyana cewa gwamnan ya samu nasara a duka qananan hukumomi 16 na faɗin jihar.
Read More
Dapo Abiodun ya lashe zaɓen Gwamnan Jihar Ogun

Dapo Abiodun ya lashe zaɓen Gwamnan Jihar Ogun

Daga SANI AHMAD GIWA Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Dapo Abiodun na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Jihar Ogun da aka gudanar ranar Asabar. Jami’in zaɓen, Farfesa Kayode Adebowale ne ya sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan kammala tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 20 na jihar. Abiodun ya samu ƙuri’u 276,298 inda ya doke Ladi Adebutu na Jam’iyyar PDP mai ƙuri’u 262,383. Biyi Otegbeye na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya zo na uku.
Read More
Sakamakon Zaɓe: Gawuna ya sha gaban Abba a Kano

Sakamakon Zaɓe: Gawuna ya sha gaban Abba a Kano

Daga BASHIR ISAH Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnoni da ya gudana ranar Asabar, a halin da ake ciki bayana sun ce ɗan takarar Gwamna na APC a Jihar Kano, Nasir Gawuna, ya sha gaban abokin hamayyarsa na NNPP, Abba Kabiru Yusuf da yawan ƙuri'u. Da fari Yusuf ne ke kan gaba da yawan ƙuri'u amma daga bisani lamarin ya juya kan Gawuna. Kawo yanzu dai INEC ta bayyana sakamakon zaɓe na ƙananan hukumomi 14 a cibiyar tattara sakamakon zaɓen. Ƙananan hukumomin su ne: Rano, Rogo, Makoda, Kunchi, Wudil, Karaye, Tsanyawa, Minjibir, Gabasawa, Ajingi, Bagwai, Kabo,…
Read More
Zaɓen Gwamna: APC tana kan gaba a ƙananan hukumomi 12 cikin 17 a Yobe

Zaɓen Gwamna: APC tana kan gaba a ƙananan hukumomi 12 cikin 17 a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Sakamakon da INEC ta fara tattarawa daga ƙananan hukumomi 12 a cikin 17 dake jihar Yobe, ya nuna jam'iyyar APC da ɗan takararta, Hon. Buni tana kan gaban jam'iyyar PDP da tazara mai yawa. Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Kwamishinan hukumar zaɓe na Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa 'yan takara 11 ne suka fafata a zaɓen daga jam'iyyun siyasa daban-daban. Ya ce a halin yanzu, INEC a Yobe ta karɓi sakamakon zaɓen kananan hukumomi 12 na gwamna a cibiyar tattara sakamakon da ke Damaturu. Gwamna Buni shi ne ɗan takarar Gwamna a jam'iyyar…
Read More