18
Mar
Daga BASHIR ISAH Mai Martaba Sarkin Keffi, Dr Shehu Chindo Yamusa II, ya yaba da yadda tsarin zaɓen wannan karon ya kankama a kan kari. Basaraken ya nuna gamsuwarsa da yadda kayan zaɓen suka iso da wuri aka kuma tantance masu zaɓe a kan kari a zaɓen gwamnoni da majalisun jihohi a ranar Asabar. Sarkin ya bayyana gamsuwarsa ne yayin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa jim kaɗan bayna kaɗa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe mai lamba 009, Tudun Ƙofa Ward da ke Ƙaramar Hukumar Keffi, Jihar Nasarawa. Ya kaɗa ƙuri’ar tasa ce da misalin ƙarfe 8:42am, tare da…