Labarai

Ganduje ya ɗage dokar taƙaita zirga-zirga a Kano

Ganduje ya ɗage dokar taƙaita zirga-zirga a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ta sanar da ɗage dokar hana fitowa da ta sa daga ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin da ta gabata. Kwamishina Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Muhammad Garba ne ya sanar da haka a daren Lahadi nan data gabata zuwa safiyar Litinin. Sanarwar ta ce duba da kwanciyar hankali da aka samu a faɗin jihar hakan ya bai wa gwamnati damar ɗage dokar ta awanni 24 da ta kafa don kare dukiya da rayukan al'ummar jihar Kwamishinan ya buƙaci 'yan kasuwar jihar da sauran masu gudanar…
Read More
An sace jami’an INEC kan hanyarsu ta zuwa cibiyar tattara sakamakon a Zamafara

An sace jami’an INEC kan hanyarsu ta zuwa cibiyar tattara sakamakon a Zamafara

Daga WAKILINMU Bayanai daga Jihar Zamfara sun ce an yi garkuwa da jami'an zaɓe a kan hanyarsu ta zuwa cibiyar tattara sakamako a yankin Ƙaramar Hukumar Maradun. Ƙaramar Hukumar Maradun nan ne mahaifar Gwmanan Jihar, Bello Mohammed Matawalle mai neman ta-zarce a shugabancin jihar. Jami'an na hanyarsu ta zuwa hedikwatar INEC da ke Gusau, babban birnin jihar, don miƙa sakamakon zaɓen gwamna na yankin Maradun. An ce bayan kama su da aka yi, an tafi da jami'an zuwa wani waje wanda ba a bayyana ba. Kakakin INEC a jihar, Muktari Janyau, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewar an sanar…
Read More
Ramadan: Ku nemi jinjirin wata gobe Laraba, kiran Sarkin Musulmi ga Musulmin Nijeriya

Ramadan: Ku nemi jinjirin wata gobe Laraba, kiran Sarkin Musulmi ga Musulmin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli Kan Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su nemi jinjirin watan Ramadan na bana bayan faɗuwar rana a ranar Laraba. Daraktan gudanarwa na Majalisar, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu, shi ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin a Abuja. Ya ce "sakamakon shawarar da Kwamitin Duban Wata na Majlisar ya bayar, Sarkin Musulmi ya buƙaci musulmin Nijeriya da su nemi jinjirin watan Ramadan na shekarar 1444 A.H. da zarar ranar ta faɗi ya zuwa ranar Laraba,…
Read More
APC a Kano ta buƙaci mambobinta su kwantar da hankalinsu

APC a Kano ta buƙaci mambobinta su kwantar da hankalinsu

Daga RABI'U SANUSI a Kano. Jam'iyyar APC reshen jihar kano ta yi kira ga 'ya'yanta su da su zama masu kara haƙuri bisa irin ta'asar da magoya bayan jam'iyyar NNPP ke yi masu da sunan murnar lashe zaɓen gwamna da ya gabata a jihar wanda ya saɓa wa doka. Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai kuma kakakin yaƙin neman zaɓen Gawuna da Garo a jihar, Malam Muhammad Garba. Sanarwar ta ce tana tabbatar wa da jama'ar jihar cewa babu abin da gwamnatin Dr Abdullahi Ganduje ke yi da ya wuce ganin ta samar wa al'ummarta…
Read More
Buhari ya koma Abuja bayan kammala zaɓen gwamnoni

Buhari ya koma Abuja bayan kammala zaɓen gwamnoni

Daga UMAR GARBA a Katsina Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan kammala zaɓen gwamnoni da na majalisar jihohi da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasar kan kafafen yaɗa labarai na zamani, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a shafinsa na sada zumunta. Yayin zaɓen, Shugaba Buhari ya kaɗa ƙuri'arsa ne a Ƙofar Baru, Sarkin Yara A, rumfa mai lamba 003 dake Daura, Jihar Katsina. Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Dikko Umar Raɗɗa ne ya lashe zaɓen Gwamna a jihar.
Read More
Mohammed Bala ya zama Gwamnan Bauchi a karo na biyu

Mohammed Bala ya zama Gwamnan Bauchi a karo na biyu

Daga BASHIR ISAH Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya ci zaɓen sake zama gwamnan jihar karo na biyu ƙarƙashin jam'iyyar PDP. Sakamakon zaɓen da Baturen zaɓen gwamna a jihar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, ya bayyana a ranar Litinin, ya nuna Gwamna Bala ya lashe ƙananan hukumomi 15 daga cikin guda 20 da jihar ke da su. Bala ya ci zaɓen ne da ƙuri'u 525,280, inda ya doke abokin hamayyarsa na APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar (mai murabus) wanda ya samu ƙuri'u 432,272.
Read More
‘Yan daba sun ƙona gidan shahararren wawaƙi Rarara

‘Yan daba sun ƙona gidan shahararren wawaƙi Rarara

Daga SANI AHMAD GIWA Bayan sa'a guda da ayyana zaɓen gwamnan jihar Kano, wasu 'yan baranda da ba a san ko su waye ba sun ƙona gidan fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara. Rarara dai ya kasance a tsakiyar matakin yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC, inda ya riƙa rera waƙa a tarurruka daban-daban yayin yaƙin neman zaɓe. Tun farko Rarara ya kasance a sansanin ɗan takarar gwamnan Kano na ADP, Sha'aban Ibrahim Sharada, kafin ya shiga tafiyar Gawuna makonni kaɗan kafin zaɓen gwamna. A cewar wani ganau wanda kuma mazaunin unguwar, Yusuf Abdullahi, ‘yan barandan ne suka shiga gidan inda…
Read More
Nasarata ta al’ummar Yobe ce – Buni

Nasarata ta al’ummar Yobe ce – Buni

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana nasarar da ya samu ta sake lashe zaɓen gwamnan jihar a matsayin babbar nasara ga daukocin al'ummar jihar amma ba tashi shi kaɗai ba. Gwamna Buni ya yi wannan furucin ne jim kaɗan bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaɓen Gwamnan jihar a ƙarƙashin jam'iyyar APC. Ya ce, “Wannan nasara ce ta ɗaukwacin al'ummar jihar Yobe, ba ni kaɗai ba." A hannu guda, Gwamna Buni ya yi kira na musamman ga 'yan hamayya da suka fafata a zaɓen…
Read More
Shugaban PDP da aka yi wa dukan kawo wuƙa a Ebonyi ya mutu

Shugaban PDP da aka yi wa dukan kawo wuƙa a Ebonyi ya mutu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban jam'iyyar PDP a Ƙaramar Hukumar Ezza ta arewa Peter Nweke, ya mutu. Nweke ya mutu ne sakamakon raunukan da ya ji bayan wasu da ake zaton ’yan dabar siyasa ne sun farmake shi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris yayin zaɓen gwamnoni da na ’yan majalisar jihohi. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ebonyi, Onome Onovwakpoyeya, ta tabbatar da mutuwar Nweke a ranar Lahadi, 19 ga watan Maris. Ta ce, an yi wa Nweke dukan tsiya sannan aka kwashe shi zuwa asibiti a cikin mawuyacin hali inda daga bisani likita ya sanar da mutuwarsa. Onome…
Read More
INEC za ta sake tattara sakamakon zaɓe na ƙananan hukumomin Adamawa

INEC za ta sake tattara sakamakon zaɓe na ƙananan hukumomin Adamawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da fom domin sake tattara sakamakon zaɓen gwamna na wasu yankuna a ƙaramar hukumar Fufore ta Jihar Adamawa. Hakan na zuwa ne bayan rikicin da ya ɓarke a ƙaramar hukumar inda ’yan bata-gari suka yi ɓarna. Kwamishinan zaɓe na jihar (REC), Hudu Yunusa-Ari, da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai a ranar Lahadi, ya ce hukumar ba ta da wani ɗan takara kamar yadda ya ce ana zarginta da shi. Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa za a bayyana wanda ya lashe zaɓen kamar…
Read More