03
Apr
Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Litinin ne kafafen yaɗa labaran Nijeriya su ka ƙaddamar da kwamitin mutane tara na hukumar sauraron ƙorafe-ƙorafen Kafafen Yaɗa Labaran Ƙasa (NMCC), wadda aka fi sani da ‘National Ombudsman’. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kabiru Yusuf, shugaban ƙungiyar ’yan jaridu ta ƙasa NPAN, kuma shugaban ƙungiyar ’yan jaridu ta Nijeriya NPO ya fitar. Yusuf ya ce, a cikin sanarwar da aka fitar ranar Juma’a a Legas, an zaɓo mambobin hukumar ne daga kafafen yaɗa labarai, malamai da ƙungiyoyin farar hula. Ya ce, matakin ya zama wajibi a yunƙurin da ake…