27
Mar
Daga SANI AHMAD GIWA Rikicin cikin gidan jam'iyyar adawa ta PDP na cigaba da zafafa, yayin da Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar PDP a gundumar Igyorov da ke ƙaramar hukumar Gboko ta Jihar Benue ya dakatar da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa Iyorchia Ayu nan take. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewa sun dakatar da Ayu ne saboda nuna adawa da jam'iyyar bayan sun kaɗa masa ƙuri'a. A lokacin da yake karanta wani ƙudiri, Sakataren jam’iyyar a gundumar Igyorov, Banger Dooyum, ya ce zagon ƙasa da Ayu tare da abokansa suka yi wa jam'iyyar ya taimaka wajen rashin yin nasarar Jam’iyyar…