28
Aug
Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana ɗaukar matakin korar wasu sojojinta biyu bisa samun su da laifin kashe malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami Gashuwa, a jihar Yobe. Sojojin da lamarin ya shafa su ne Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon. Sanarwar korar ta fito ne daga muƙaddashin kwamandan da ke kula da Bataliya ta 241 dake Nguru a jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, inda ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin binciken haɗin gwiwa da aka kafa tare da haɗin gwiwar 'yan sanda ya same su da laifi. Ya ƙara da…