15
Aug
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Bashir Ahmad matsayin Hadimi na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Sadarwa na Zamani. Sanarwar naɗin na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya aikawa Bashir ɗin mai ɗauke da kwanan watan 20 ga Yulin 2022. Kafin wannan lokaci, Bashir Ahmad shi ne hadimin Shugaba Buhari kan sabbin kafafen yaɗa labari inda ya ajiye muƙamisan don yi takarar ɗan Majalisar Wakilai. Cikin wasiƙar da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya gani, sabon muƙamin da Buhari ya bai wa Bashir zai fara aiki ne daga ranar 19 ga watan Yulin…