Ra’ayi

Shin ana sane ake bawa ‘yan shaye-shaye mafaka a gwamnatance da siyasance?

Shin ana sane ake bawa ‘yan shaye-shaye mafaka a gwamnatance da siyasance?

Daga AMB. AUWAL MUHAMMAD ƊANLARABAWA Ni Amb Auwal Muhd Ɗanlarabawa, ina kira a kan shugabanni da hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a kan a kawo ɗauki wuraren da ake shaye-shaye kamar sakatariyar ƙananan hukumomi da ma'aikatun gwamnati da sauran wuraren taruwar 'yan siyasa don magance ta'ammali da kayan maye. Ni a ganina, da yawa ana kokawa da yadda matasa ke amfani ma'aikatun Gwamnati da wuraren da ake hada-hadar siyasa tare da fakewa ana shaye-shaye, wanda ba mai hanawa ballantana saka doka ta hana su cigaba da aikata laifuka. Hakazalika, Masu kawo ƙorafi sun bayyana cewa idan aka…
Read More
GAMJIK 2022: Yadda marubutan adabi suka ɗaura ɗamarar yaƙi da rubutun batsa

GAMJIK 2022: Yadda marubutan adabi suka ɗaura ɗamarar yaƙi da rubutun batsa

Na samu gayyata ta musamman daga ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Kano wato GAMJIK ta hannun abokina kuma marubuci Mansur Usman Sufi, bayan gayyatar da aka yi wa wasu ƙungiyoyin marubuta da nake jagoran ta, waɗanda kuma har wa yau suna daga cikin ƙungiyoyin da suka shiga Gasar Muhawara da GAMJIK ta shirya, domin ƙara ƙarfafa zumunci a tsakanin marubutan adabin Hausa, da ba da gudunmawa a ɓangarorin cigaban rayuwa. Babu shakka taro ya ƙayatar sosai, kuma an gudanar da shi cikin nasara, saboda yadda aka samu halartar dandazon marubuta daga sassan arewacin ƙasar nan, tsofaffin marubuta, matasa masu tasowa, manazarta…
Read More
Auren ‘yar boko!

Auren ‘yar boko!

Daga AMINA YUSUF ALI 'Yar boko! Wannan shi ne sunan da ake kiran macen da ta yi karatu kuma take yin aiki ko take karatun gaba da Sakandare, ko ta gama, ko tana aikin albashi ko ma ba ta aikin. Wannan shi ne lissafin kuɗin goro da ke wa mace 'yar boko a ƙasar Hausa. Masu karatu barkanmu da haɗuwa a wani makon mai albarka! Ta cikin jaridarku mai farin jini, Manhaja. A yanzu kuma za mu tsunduma kan maudu'inmu na wannan mako. A kan auren 'yar boko da irin abubuwan da suke tattare da auren. Duba da yadda a…
Read More
Tallafa wa mazauna karkara a matsayin matakin rage talauci na Ma’aikatar Jinƙai

Tallafa wa mazauna karkara a matsayin matakin rage talauci na Ma’aikatar Jinƙai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A kwanakin baya ne Ma’aikatar Jin Ƙai da Kula da Bala’o’i da Ci Gaban Jama’a ta Tarayya (FMHADMSD) ta fara rabon tallafin kuɗi Naira 20,000 ga matan karkara 2,900 a babban birnin tarayya da sauran sassan ƙasar nan a ƙarƙashin shirinta na ‘National Social Investment Programs’ (NSIP), domin rage talauci ga ɗaukacin al'ummar Nijeriya. Ga mafi yawan 'yan Nijeriya, ma’aikatar jin ƙai da kula da bala’o’i da ci gaban jama’a ta tarayya (FMHADMSD), ta kasance mafi kyawun abin da 'yan ƙasa ke alfahari da shi a sakamakon shirye-shiryenta da suka shafi mutane da yawa. Tun farkon…
Read More
Nasiha ga matan da za a yi wa kishiya

Nasiha ga matan da za a yi wa kishiya

Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabin Rahma, Muhammad (SAW). Ki zama mai mayar da al'amuranki ga sarki Allah, shi ne ya zama gatanki majiɓincin al'amuranki, in ki ka yi haka, kin tsira daga zuwa wajen bokaye da ’yan duba don ƙulla makirci. Ki kasance mai yarda da ƙaddara domin kuwa tuntuni Allah ya hukunta za ku zauna ƙarƙashin miji ɗaya. Ki sanya wa ranki cewar mijinki ya yi riƙo ne da sunnar Annabi SAW. Ki zama mai haƙuri saboda Allah, ba mai haƙurin tilas ba. Karki takurawa mijinki a kan…
Read More
Muhimmancin zama mutumin kirki

Muhimmancin zama mutumin kirki

Masu karatu, assalamu alaikum. A wannan makon za mu duba wani sabon maudu’in ne na daban. Wato bayani game da halayyar zama da abokai da ƙawaye. Dalili ke nan ma kanun madu’in namu ya yi tambaya, shin ko kana son zama mutumin kirki a rayuwarka? Ke ma ’yar uwa, ko kina son ki zama mutunniyar kirki a rayuwarki ta duniya? To ku biyo ni a cikin wannan madu’i, domin ganin matakan da suka kamata mu ɗauka, mu aiwatar a rayuwarmu ta yau da kullum, domin ganin mun cimma matsayin zama na kirki a rayuwa. A rayuwa, ɗan Adam ba zai…
Read More
Kawar da ciwon hanta kafin 2030

Kawar da ciwon hanta kafin 2030

A baya-bayan nan ne ƙasashen duniya suka gudanar da bikin ranar yaƙi da cutar Hepatitis wanda ake kira da ciwon hanta a Hausance, domin ƙara wayar da kan jama’a game da wannan mummunar cuta da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka haɗa da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta nau'in B da C a duniya. A yayin da ciwon hanta nau'in B kawai ke lashe…
Read More
Dauda Kahutu Rarara: Zakaran da Allah Ya nufa da cara

Dauda Kahutu Rarara: Zakaran da Allah Ya nufa da cara

Daga KWAARED ABDU ZANGO Haƙiƙa Allah shi ne gwani kuma mai ba wa kowa arziƙin da ya so ta hanyoyin da ɗan adam ya yanke ƙauna. Gaskiya ne akwai mawaƙa da yawa cikin duniyagga kuma ana ganin arziƙin da Allah Ta’ala yayi masu ta hanyar sana’ar waƙa. Bari kawai mu duƙufa kawai a Nijeriya ta Arewa inda take da mawaƙa shahararru waɗanda sun yi fice sosai a duniyar waƙoƙin Hausa, kususan na zaɓe da masu sa hikimar su kaɗaita kotso, molo, garaya, kuntigi, goge da dai sauransu kamar kiɗan ɗanmaraya da mai irin muryarsa ɗan zamfara Babangida Kakadawa. To cikin…
Read More
Wai haka za mu zauna?

Wai haka za mu zauna?

Daga MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI FAGGE Ka ga mutum ya zo nan ƙiri-ƙiri yana ta haƙilon tsine wa Obasanjo ko Buhari ko Jonathan da sauransu amma sai ka gan shi in ɗalibi ne, an zana masa NECO ko WAEC ta hanyar cuwa-cuwa a "miracle centre" ko kuma ba shi da takardu na gaskiya, duk babu ne, ya biya an yi masa na ƙarya. Ko kuma ka gan shi ko ka gan ta a jami'a tana satar amsa, ko kuma a haɗa baki da shi a ƙara kuɗin da za a amsa a wajen babansa. Idan magidanci ne yana koyarwa a jami'a…
Read More
Matsalar rashin tsaro; ɗan leƙen asiri ya fi ɗan ta’addar daji iya ta’adanci…

Matsalar rashin tsaro; ɗan leƙen asiri ya fi ɗan ta’addar daji iya ta’adanci…

Daga MUHAMMAD AMINU KABIR Lamarin rashin tsaro yana ƙara ƙamari ne ta sanadiyyar wasu daga cikin Al'umma da har yanzu suke ɗaukar bayanan sirri ko dai na jama'ar gari, ko kuma na Jami'an tsaro suna kai wa varayin daji. Wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa lamarin nan ya ƙi ci, ya qi cinyewa. A kullum Jami'an tsaro suna bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an magance wannan matsalar ta rashin tsaro, amma kuma wasu ɗaiɗaikun mutane da rashin tsoron Allah ya hana su barin wannan mummunar ɗabi'ar ta ɗaukar bayanai su kai wa 'yan ta'adda. Abin takaici baka iya…
Read More