Ra’ayi

Arewacin Nijeriya: Tauyayyun Zakuna (2)

Arewacin Nijeriya: Tauyayyun Zakuna (2)

Daga MUHAMMAD NASEER LERE Kamar yadda na bayyana mana irin halin da muka tsinci kan mu a arewa a kashi na farko, har na kawo yadda masu yi mana aikace-aikace da biya mana buƙatu na yau kullum suka rikiɗa, suka koma masu nema mana mafitar yanayin da ko dabbobi da gonakin Arewa bai ƙyale ba. Sannan na tsakura muku yadda suka yanke cewa za su fito su nuna irin yadda aka siyasantar da harkar tsaro a yankin Arewa. Wataƙila sun zavi wannan matakin ne domin sun san cewa, 'yan Arewa suna da hakkin rayuwa cikin annashuwa da walwala kamar yadda…
Read More
Sasanci tsakanin Hausawa da Fulani zai magance matsalar tsaro a Arewa

Sasanci tsakanin Hausawa da Fulani zai magance matsalar tsaro a Arewa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ashe matsalar tsaro da ake fama da ita a Arewa, na da nasaba da kisan ƙare dangi da Fulani ke yi wa ƙabilar Hausawa? Tun da ake samun ƙalubalen tsaro a jihohin Arewa maso yammacin Nijeriya tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa manoma, ban taɓa kawo wannan tambayar a raina ba, don ina ganin ba batun kisan ƙare dangi ba ne, tsohuwar rigima ce da aka saba fuskanta tsakanin manoma da makiyaya, ƙalubalen ɗumamar yanayi da ya kai ga cinye burtalolin shanu zuwa filayen gonaki, da kuma uwa uba shigar ɓata gari cikin harkar satar shanu da…
Read More
Ɗaukar nauyin iyali: Taimakon da ya wajaba a kan mace

Ɗaukar nauyin iyali: Taimakon da ya wajaba a kan mace

Daga AMINA YUSUF ALI Idan mai karatu bai manta ba, a makon da ya gabata, mun tattauna a kan haƙƙoƙin iyali da kuma wasu dalilai da suke hana maza kasa sauke wannan nauyi da Allah ya raba ya ɗora musu. Su ma mata Allah ya ɗora musu nasu haƙƙoƙin. Sai dai abin lura kusan dukkan ko ma dukka haƙƙoƙin da suka shafi ɗaukar nauyi ta fuskar kuɗi maza Allah ya ɗora wa. Sai dai wani lokacin maza kan bar wa mata wannan ragamar ba tare da tunani ko yardar ta ba. Wata kuma ba yardar tata amma ta karɓa don…
Read More
Ruwan tumfafiya: Tattaki a yanar gizo, leƙe cikin zaurukan ‘Yahoo Groups’

Ruwan tumfafiya: Tattaki a yanar gizo, leƙe cikin zaurukan ‘Yahoo Groups’

Tattarowa: Khalid Musa Hausawa su ka ce kishi kumallon mata. Duk da cewa ba mata ne kawai su ka kaɗaita da halittar kishi ba, mazaje ma a nan ba su tsira ba amma ya fi shahara ga mata domin karancin juriyarsu gare shi. Wannan muhawara ta Ruwan Tumfafiya an yi ta ne a kan Kishi ko Kishiya. Wata Marubuciya Salamatu Adamu ita ce ta haifar da wannan muhimmiyar Muhawar a dandalin Marubuta na Yahoo wacce ta samu gudunmawar wasu hazikan Marubuta da su ka ja zaren muhawar abinda ya kara ma ta armashi. Wadannan Marubuta sune: Habibiy, Muhammad Fatuhu Mustapha…
Read More
Dandalin shawara

Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Anty Asas don Allah ki taimaka min da shawara. Wallahi Ina cikin tashin hankali da kuma rashin madafa. Anty ƙanwata ce ta yi cikin shege. Hankalinmu ya tashi sosai har mu ka rasa inda za mu yi da lamarin. Sai dai cikin kwanakin da wannan lamari ya faru, sai na lura, mijina da mahaifiyata na yawan keɓewa. Idan suna magana kuwa da na shigo wurin da suke sai su yi shiru. Abin tun ba ya damuna har ya zo ya fara. Ana cikin haka kuma sai mahaifiyar tamu ta zo ta daina maganar cikin…
Read More
Maraba da shekara ta Hijira 1444

Maraba da shekara ta Hijira 1444

Bayan godiya da yabo ga Allah. Ina amfani da wannan dama mu faɗakar wa junanmu cewa zuwan shekara ta Hijira 1444 wata alama ce mai nuna a kullum muna bankwana da wannan duniya kuma muna fuskantar tafiya ga rayuwa ta har abada wacce ake guzurinta tun a nan duniya. Tabbas al'ummar Musulmai mu na da manyan ƙalubalai a rayuwa wanda ba kowa ke gane hakan ba sai wanda Allah ya haska ma wa. Haɗin kai da taimakekeniya a yau sun wuyata. Inda rarrabuwa da kuma rashin daraja juna ta yawaita. Da fatan inda duk Musulmai muke da yawan bayyana matsalolin…
Read More
Batun haramta babura da haƙar ma’adanai a faɗin Nijeriya

Batun haramta babura da haƙar ma’adanai a faɗin Nijeriya

A wani yunƙuri na shawo kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a ƙasar, gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta na sanya dokar hana amfani da babura da ma’adanai a faɗin tarayyar ƙasar nan. Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya bayyana hakan kwanan nan. A cewarsa, irin wannan matakin zai kawar da hanyoyin samun kuɗaɗe ga 'yan ta'adda da kuma 'yan fashin daji a Nijeriya da ke amfani da kuɗaɗen da ake samu daga waɗannan kafofin wajen ƙarfafa ayyukansu na aikata laifuka. Malami ya ci gaba da cewa, waɗannan kayan aikin da ’yan ta’addan ke…
Read More
A ceto fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna!

A ceto fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ni dai duk waɗanda su ka yi min magana bayan kallon faifan bidiyon da ’yan ta’addan da su ka sace fasinjojin jirgin ƙasa kan hanyar Abuja zuwa Kaduna su ka fitar, sun nuna juyayi da kaduwa kana bun da su ka gani. Cin zarafin da ’yan ta’addan su ke yi wa fasinjojin ko ma za a ce farafagandar batawa gwamnati rai ce, amma da ban takaici ainun. Mutane masu ’yanci waɗanda laifin su kaɗai shi ne sun shiga jirgin ƙasa su na nufin sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna amma wasu su ka kai mu…
Read More
Arewacin Nijeriya: Tauyayyun zakuna!

Arewacin Nijeriya: Tauyayyun zakuna!

Daga MUHAMMAD NASEER LERE Ba ƙaramin lamari ba ne ballantana a ce zai iya shiga rubibi har a manta. Na tabbata komai nisan lokaci ƙwaƙwalenmu ba za su iya mantawa da irin kisan gillar da ake mana a AREWA ba! Sannan ba za mu iya hana bakunanmu faɗin, An kasa ceto rayukanmu ba. Ina tunanin muna faɗin hakan ne domin kunnuwanmu sun ji lokacin da gwamnatinmu ke rantsuwar tsare rayukanmu. Kenan, ba za mu iya daina faɗin, an kasa ceto rayukanmu ba, har sai ranar da muka manta da kalaman gwamnati na alƙwarin tsare dukiya da rayukanmu. Ko dai mu…
Read More
Tsaftace yadda matasa ke amfani da zaurukan sada zumunta

Tsaftace yadda matasa ke amfani da zaurukan sada zumunta

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ƙarshen makon da ya gabata na samu halartar wani babban taron bita na yini biyu da ƙungiyar matasan Arewa masu amfani da zaurukan sada zumunta don isar da saƙonni, yaɗa labarai da tallata kayayyakin su na kasuwanci ta gudanar. Ƙungiyar da aka fi sani da suna Arewa Media Writers, ta shirya gagarumin bikin cika shekaru biyu da kafuwar ƙungiyar ne a garin Bauchi, wanda ya gudana a babban Hotel ɗin nan na Zaranda. Matasa daga dukkan sassan jihohin Arewa sun samu halartar wannan taro, wanda aka yi wa taken 'Rawar Da Kafofin Sada Zumunta Ke…
Read More