21
Jul
Daga SALMAN MUKHTAR A kwanakin baya an kai hare-hare guda biyu da suka ɗauki hankalin mutanen Najeriya, waɗanda sun ƙara fito da asalin ƙarfin 'yan ta'adda da kuma nuna yatsa ga ƙarfin jami'anmu. Hari na farko, shi ne wanda aka kai gidan gyaran hali na Kuje (Abuja), inda waɗannan maciya amanar ƙasa su ka yi ta harbe-harbe tare da ɓalle wannan magarƙama, in da rahotanni suka nuna aƙalla kashi 90% na mutanen da ke ciki sun tsere. A cikin wanda aka nema aka rasa a wannan magarƙama, har da tsohon jami'in ɗan sanda, Abba Kyari, da ake tuhuma da laifin…