15
Oct
Sanarwar da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi kan cewa, ya amince da ware Naira biliyan 13.3, don fara aikin 'yan sanda na al'umma a cikin jihohi 36 na ƙasar da Babban Birnin Tarayya Abuja yana nuna jajircewar shugaban wajen tabbatar da cewa, ya yi duk abin da ya yi alƙawarin zai aiwatar kafin ya bar gadon mulki. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja a wani taron bita na kwanaki biyu na duba ayyukan Ministoci wanda aka shirya don tantance ci gaban da aka samu don cimma muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba,…
