27
May
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Barcelona da Jordi Alba sun cimma yarjejeniyar raba gari tun kan kwantiraginsa ya ƙare a ƙungiyar. Alba, mai shekara 34 ya koma Camp Nou a 2012 daga Valencia, ya kuma lashe La Liga shida da Copa del Rey biyar da gasar Zakarun Turai a 2015. Ya buga wa Barcelona wasanni 458 har da 29 a kakar nan da ƙungiyar Camp Nou ta ɗauki La Liga na bana na 27 jimilla. Alba ya zama na biyu da zai bar Barcelona a aarshen kakar nan, bayan kyaftin, Sergio Busquets. Barcelona ta kai ga cimma wannan matsaya, bayan da…