03
Feb
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mai tsaron bayan tawagar ƙwallon ƙafar Faransa da kuma ƙungiyar Manchester United, Raphael Varane, ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa ƙwallo. Ɗan wasan wanda ya lashe kofin duniya a 2018, ya ci wa Faransa ƙwallaye biyar a wasanni 93 da ya buga tun daga 2013. Wasansa na ƙarshe shi ne wasan ƙarshe na kofin duniya a Qatar 2022, wanda suka yi rashin nasara a hannun Argentina. "Wakiltar ƙasata na tsawon lokaci shi ne babban karamcin da na samu a rayuwata," inji Varane. Ya ƙara da cewa, "a duk lokacin da na saka shuɗiyar…