Kasashen Waje

Za mu hukunta ƙasashen da suka bijire wa yaƙi da ɗumamar yanayi – MƊD

Za mu hukunta ƙasashen da suka bijire wa yaƙi da ɗumamar yanayi – MƊD

Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ɗaukar wani mataki da zai fara hukunta ƙasashen da ke fitar da hayaƙi da sinadaran da ke gurɓata muhalli ba kuma tare da ɗaukar matakin da ya dace ba. A wata ƙuri’ar jin ra’ayi tsakanin ƙasashe mambobin majalisar mai cike da tarihi da aka kaɗa a ranart Laraba, da tsibirin Vanuatu ya bada shawara, ta kuma tanadi damar gurfanar da ƙasar da aka samu da saɓa wannan doka, gaban kotun duniya musamman idan wannan ƙasa ta yi kunnen ƙashi wajen bada gudunmawa a yaƙi da gurvatar muhalli. Da yake jawabi bayan kaɗa ƙuri’ar, Firaministan…
Read More
Mahajjatan Umarah 20 sun rasu, 29 sun jikkata a hatsarin mota a Makka

Mahajjatan Umarah 20 sun rasu, 29 sun jikkata a hatsarin mota a Makka

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Saudiyya sun ce, wasu mahajjatan Umarah su 20 sun riga mu gidan gaskiya, sannan 29 jikkata sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a Makka. Bayanai sun ce mahajjatan sun gamu da wannan jarrawar ce a kan hanyarsu ta zuwa aikin Umara a Makka a ranar Litinin. Wata majiya ta ce mai yiwuwa adadin waɗanda suka rasa ransu ya ƙaru duba da yanayin raunukan da wasunsu suka ji. Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da 'yan asalin Saudiyya da kuma baƙi daga sauran sassan duniya da suka tafi Saudiyya don yin Umarah. An…
Read More
Sanatoci sun fatattaki sanatan da bai taɓa halartar zaman majalisa ba

Sanatoci sun fatattaki sanatan da bai taɓa halartar zaman majalisa ba

’Yan majalisar Japan sun kori wani sanata daga Majalisar Dattawan ƙasar bayan ya kwashe wata bakwai bai halarci zaman majalisar ba. Sanatan, wanda fitacccen mai amfani da shafin YouTube ne, ya zama ɗan majalisa na farko da aka kora ba tare da ya tava shiga zauren Majalisar Dattawan ba tun da aka zaɓe shi. Sanatocin sun kori Sanata Yoshikazu Higashitani ne a ranar Talata sakamakon rashin halartar zaman majalisar. Tunda aka zaɓe shi wata bakwai da suka gabata, ko sau daya bai taɓa halartar zaman majalisar ba. Kwamitin Ladabtarwa na majalisar ne ya yanke hukunci korarsa saboda ci gaba da…
Read More
Rashin haɗuwar tawagar alƙalan New York ya tilasta ɗage tuhumar Trump

Rashin haɗuwar tawagar alƙalan New York ya tilasta ɗage tuhumar Trump

Batun tuhumar da ake yiwa tsohon shugaban Amurka Donald Trump a game da bai wa wata jarumar fina-finan batsa maƙudan kuɗaɗe a matsayin toshiyar baki don kada ta tona abin da ta ce ya taɓa shiga tsakaninsu ya ɗauki sabon salo a ranar Laraba, bayan da tawagar alƙalan birnin New York ta gaza zama kamar yadda aka yi tsammani, lamarin da ya tilasta ɗage yanke hukuncin zuwa mako mai zuwa. Tun bayan da tsohon shugaban na Amurka Donald Trump da kansa ya sanar da cewa ana shirin kama shi a wannan makon, lamarin da ya sanya raɗe-raɗin yiwuwar gurfanar da…
Read More
An kama mabaraci da tsabar kuɗi Naira miliyan 37.3 ɓoye cikin ƙafafun roba

An kama mabaraci da tsabar kuɗi Naira miliyan 37.3 ɓoye cikin ƙafafun roba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jami’an ’Yan Sandan Dubai sun kama wani mabaraci da ya bayyana a matsayin wanda aka yanke wa ƙafa, ɓoye da tsabar kuɗi $81k kwatankwacin Naira miliyan 37.3 a cikin jabun ƙafafun roban. A cewar jaridar Gulf News, mutumin da ya shiga ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da takardar bizar ziyara an kama shi ne a ranar Alhamis 16 ga Maris, 2023, inda yake roƙon sadaka a kusa da masallatai da kuma wuraren zama. An tattaro cewa mabaracin bayan kama shi an miƙa shi zuwa gaban kotu na Dubai. ’Yan sandan Dubai sun gargaɗi jama’a da kada su…
Read More
MƊD da Ukraine sun buƙaci tsawaita yarjejeniyar da aka ƙulla da Rasha

MƊD da Ukraine sun buƙaci tsawaita yarjejeniyar da aka ƙulla da Rasha

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy da Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres sun yi kira da a tsawaita yarjejeniyar da aka ƙulla da gwamnatin Moscow wadda ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsi ta tashar ruwan tekun Black Sea. Shugaban na Ukraine ya jadaddawa Guterres a birnin Kyiv cewa shirin samar da hatsin yana da matuƙar muhimmanci ga duniya, da kuma sassauta farashin abinci a duniya. Yarjejeniyar ta kwanaki 120 da Majalisar Ɗinkin Duniya da Turkiyya suka ƙulla tun a watan Yulin da ya gabata kuma aka tsawaita a watan Nuwamba, za a sabunta ta ne a ranar 18…
Read More
Narendra Modi ya buƙaci haɗin kai don kawo ƙarshen yaƙin Ukraine a taron G20

Narendra Modi ya buƙaci haɗin kai don kawo ƙarshen yaƙin Ukraine a taron G20

Firaministan Indiya Narendra Modi ya buƙaci haɗin kan ƙasashe da kawo ƙarshen rarrabuwar kan da yaƙin Ukraine ya haddasa wanda ya ce yana ƙoƙarin jefa duniya a gagarumar matsala, dai dai lokacin da ake buɗe taron ƙasashe 20 mafiya ƙarfin tattalin arziki da ƙasar ke karbar baƙonci. A jawabinsa wajen bikin buɗe taron ƙasashe 20 mafiya ƙarfin tattalin arziki da ke gudana birnin New Delhi, Modi ya ce idan aka duba matsalolin da aka fuskanta a fannoni da dama kama daga tattalin arziki qarancin abinci da kuma hada-hadar kuɗi baya ga sauyin yanayi da kuma ƙaruwar ayyukan ta’addanci a shekarun…
Read More
An bankaɗo asirin wani kamfanin Isra’ila da ya shahara wajen sauya zaɓen ƙasashe

An bankaɗo asirin wani kamfanin Isra’ila da ya shahara wajen sauya zaɓen ƙasashe

Wasu kamfanonin yaɗa labaran ƙasashe, sun yi haɗin gwiwa wajen bankaɗo ayyukan wani kamfani da aka yi wa laƙabi da Team George wanda ya ƙware wajen murɗa zaɓe da kuma yada farfagandar da za ta tayar da tarzoma a zaɓuɓɓukan ƙasashen duniya. Bayan kafar yaɗa labaran da ta gudanar ta gano cewa kamfanin na shirin Murɗa labarai sama da 30 afaɗin duniya, cikin ƙasashen da ke shirin zaɓe a baya-bayan nan. Kamfanin mallakin tsohon sojan ƙasar ta Isra’ila Tal Hanan mai shekaru 50, ya ƙware wajen murɗa zaɓuɓɓuka ta hanyar shiga rumbunan tattara sakamakon zaɓen hukumomin zaɓe da kuma aringizo…
Read More
Girgizar ƙasar Siriya-Turkiyya: Yawan matattu ya kai 5000, gidaje 5775 sun rushe

Girgizar ƙasar Siriya-Turkiyya: Yawan matattu ya kai 5000, gidaje 5775 sun rushe

Daga BASHIR ISAH Kawo yanzu, kimanin mutum 5,000 aka tabbatar sun mutu, wasu dubbai sun jikkata a girgizar ƙasar da ta auku a Turkiyya da Siriya a ranar Litinin. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Mataimakin Shugaban Ƙasar Turkiyya, Fuat Oktay, da safiyar ranar Talata. Ya ce mutum 3,419 sun mutu yayin da 20,534 sun jikkata a Turkiyya. A ɓangaren Siriya kuwa, yawan waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 1,602, wanda baki ɗaya jimillar ta kama 5,021. Hukumar kula da iftila'i ta ƙasar Turkiyya, ta ce rahotanni sun nuna gidaje 11,342 girgizar ta shafa, amma gidaje 5,775 ne aka…
Read More
Sama da mutum 1,800 sun mutu a girgizar ƙasar Turkiyya da Siriya

Sama da mutum 1,800 sun mutu a girgizar ƙasar Turkiyya da Siriya

Daga BASHIR ISAH Aƙalla mutum 1,800 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta auku a Turkiyya da Siriya. Iftila'in wanda ya auku da safiyar Litinin, ya lalata wasu manya biranen Turkiyya, yankunan da galibin 'yan gudun hijira daga Siriya ke da zama. An ga masu aikin ceto na ta ƙoƙarin bincike don gano mutanen da ƙasa ta rufta da su. Rahotanni sun ce wannan ita ce girgizar ƙasa mafi munin da aka fuskanta a baya-bayan a yankunan da lamarin ya shafa. Tuni ƙasashe duniya irin su Chana, Indiya, Qatar, Amurka da sauransu suka bayyana ƙudirinsu na tallafa…
Read More