21
Jan
Daga AMINA YUSUF ALI Festus Keyamo, mai magana da yawun majalisar kamfe ta jam'iyyar APC, ya shigar da ƙara a kan hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), yana neman kotu ta kama Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP na shugabancin Nijeriya. A cikin ƙarar, Festus Keyamo wanda lauya ne mai muƙamin SAN ya haɗa da dokar Hukumar daƙile laifukan cin hanci da makamantansu (ICPC) Hukumar kula da dokar ɗa'ar aiki (CCB) a cikin ƙarar, bayan wa'adin awoyi 72 da ya bayar sun cika. Keyamo, lauya mai muƙamin SAN, ya ba da…