27
Dec
Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da kashe wata lauya da ’yan sanda suka yi a ranar Kirsimeti a Jihar Legas. Buhari ya ce, ya yi matuƙar kaɗuwa da kisan Omobolanle Raheem, tare da bai wa hukumaomin ‘yan sanda umarni kan ɗaukar matakin da ya dace a kan waɗanda suka yi aika-aikar. Shugaban ya ce, wannan manuniya ce kan yadda ake mu'amala da bindigogi ba yadda ya dace ba. Ya ƙara da cewa, faruwar al’amarin fargarwa ce ga hukumomi ciki har da hukumar ‘yan sanda kan aiwatar da tsare-tsaren da ake da su dangane da…