04
Dec
Daga UMAR GARBA a Katsina 'Yan bindiga sun yi dirar mikiya a wani masallaci dake garin Maigamji a Ƙaramar Hukumar Funtua a dai-dai lokacin da ake gabatar da Sallar Issha'i. Wani mazaunin garin ya shaida wa majiyar Manhaja cewa, da zuwan ɓarayin ana tsaka da Sallah sai suka buɗe wuta inda nan take suka harbi mutane biyu ciki har da wanda rahotanni suka ce shi ne limamin dake jan Sallar. Wanda yanzu haka suna karɓar magani a babban asibitin garin funtua. Rahotannin dai sun bayyana cewar, maharan sun yi awon gaba da mutane da dama. Harin na zuwa ne bayan…