Labarai

Abduljabbar: Za mu ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisa – Ƙungiya

Abduljabbar: Za mu ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisa – Ƙungiya

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Wata ƙungiya ƙarƙashin ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Alhaƙƙu ta bayyana shirinta na ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisa da kotun shari'a ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Kabara bisa samunsa da laifin ɓatanci. Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Juma'a a Kano, shugaban ƙungiyar Sa'id Bn Usman, ya bayyana cewa ƙungiyar ta tattaunawa da iyalai da makusantan malamin kan batun, kana daga bisani sun yanke shawarar ɗaukaka ƙara domin tabbatar da adalci. Ya ƙara da cewa, ƙungiyar ba ta gamsu da hukuncin ƙaramar kotun ba. A cewarsa, an kammala shirin ɗaukaka ƙarar nan…
Read More
Gwamnati ta ayyana ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara

Gwamnati ta ayyana ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 26 da 27 ga Disamba, 2022 da kuma 2 ga Janairun 2023 a matsayin ranakun hutun gama-gari. Gwamnati ta ba da hutun ne albarkacin bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara. Ta ce 26 da 27 ga Disamba hutu ne don Kirsimeti da 'Boxing Day', yayin da 2 ga Janairu take hutu don bikin sabuwar shekarar 2023. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya fitar ranar Juma'a ta hannun Babban Sakataren Ma'aikatar, Dr. Shuaib M.L. Belgore. Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen taya…
Read More
Rikicin makiyaya da manoma ya yi sanadin ƙonewar gidaje 15 a Guri

Rikicin makiyaya da manoma ya yi sanadin ƙonewar gidaje 15 a Guri

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Rikici tsakanin makiyaya da manoma a ƙauyen Sakasza dake cikin yankin Ƙaramar Hukumar Guri a Jihar Jigawa ya yi sanadin ƙonewar gidaje 15 daga ɓangarori biyu na abokan faɗar. Rikichin ya faru ne sakamakon ta'adi da Fulanin suka yi wa manoma a gonakinsu a cikin makon da ya gabata, inda Fulani makiyaya suka sanya shanu a gonakin manoman da tsakiyar rana suka cinye masu amfanin gona. Hakan ya sa manoman na ƙauyen Sakasza suka ɗauki makamai suka yi wa rugagen Fulanin na Sakasza tsinke suka ƙone masu bukkokinsu suka fatattaki Fulanin daga rigagensu. Sakamakon…
Read More
INEC ta koka: ’Yan siyasa na sayen katin zaɓe

INEC ta koka: ’Yan siyasa na sayen katin zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce, wasu ’yan siyasa su na sayen Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) daga hannun masu kaɗa ƙuri'a. Mohammed Haruna, muƙaddashin kwamishinan INEC na ƙasa mai kula da babban birnin tarayya Abuja, Nasarawa, Kaduna da Filato, ya bayyana haka a ranar Litinin yayin ƙaddamar da shirin ‘VoteMatters’ na NESSACTION a Abuja. Kamar yadda aka ruwaito, Haruna ya ce, hukumar zaɓe na kai farmaki kan ’yan kasuwar bayan fage masu sayar da Katin Zaɓe. “Muna sane da cewa wasu ’yan siyasa sun duƙufa sayen katunan zaɓe. Ba daidaj bane…
Read More
Gwamnati ta amince da sabon ƙudirin dokar fallasa ɓarayin gwamnati

Gwamnati ta amince da sabon ƙudirin dokar fallasa ɓarayin gwamnati

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta amince da sabuwar dokar kwarmato don fallasa ɓarayin gwamnati. Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ce ta amince da dokar yayin zamanta na ranar Laraba. A cewar Gwamnati, dokar za ta taimaka mata wajen ci gaba da yaƙi da rashawa a ƙasar nan. Da take yi wa manema labarai ƙarin haske game da zaman Majalisar, Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed ta ce: “Ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare ta gabatar da ƙudurori da dama a yau.” Ta ce daga ciki har da dokar fallasa ɓarayin gwamnati ta 2022. Ta ce dalilin wannan doka shi ne don ƙarfa…
Read More
Kotu ta janye umarnin tsare Usman Baba

Kotu ta janye umarnin tsare Usman Baba

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Abuja ta janye umarnin da ta bayar kan tsare Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Usman Baba a gidan yari. Hakan ya biyo bayan tabbacin da ya bayar ne kan cewa Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ƙarƙashin kulawarsa, za ta za zamo mai ɗa’a da biyayya ga dokoki da kare ’yancin ’yan ƙasa. Kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a Bolaji Olajuwon, ta janye umarnin nata a kan Baba ne yayin zaman da ta yi ranar Laraba. Tuni Sufeto-Janar ɗin ya yaba wa kotun bisa janye umarninta a kansa. Tun farko, Kotu ta ba da umarnin tsare Baba a kurkuku na…
Read More
‘Yan Nijeriya miliyan 25 za su shiga matsalar ƙarancin abinci a 2023 – FAO

‘Yan Nijeriya miliyan 25 za su shiga matsalar ƙarancin abinci a 2023 – FAO

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), ta bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 25.3 za su fuskanci mummunan matsalar ƙarancin abinci a tsakanin watannin Yuni da Agustan 2023. A cikin sanarwar da FAO ɗin ta fitar, ta ce idan tun da wuri ba a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki ba, to mutum miliyan 4.4 a Barno, Adamawa da Yobe za su rasa cin yau da na gobe. Cikin rahoton da hukumar ta fitar na watan Oktoba 2022, FAO ta ce a yanzu haka mutum miliyan 17 na rayuwar cin abincin da kwata-kwata ba mai…
Read More
Babu laifin mu a wahalar man fetur da a ke yi a Nijeriya – IPMAN

Babu laifin mu a wahalar man fetur da a ke yi a Nijeriya – IPMAN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Dillalan Man fetur ta Ƙasa, IPMAN, ta fitar ce ba laifinta ba ne a ƙarancin man fetur da ake fama da shi a ƙasar. Ƙungiyar ta kuma ce mambobinta ba su da hannu a ƙarancin da ake fama da shi a halin yanzu. Femi Adelaja, Shugaban IPMAN ta defot ɗin Mosinmi a Jihar Ogun, a wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen mako, ya ce babu man fetur a cikin gidajen man fetur na ƙasa (NNPC) a faɗin Nijeriya. Ya ce a yanzu haka farashin man fetur daga defot ya kai Naira 220…
Read More
Na’urorin BVAS da sauran muhimman kayan zaɓe na nan lafiya ƙalau — INEC

Na’urorin BVAS da sauran muhimman kayan zaɓe na nan lafiya ƙalau — INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa, ba a ajiye na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) a wuraren da 'yan bangar siyasa su ka kai hari tare da ƙona su kwanan nan ba. INEC ta kuma ce wasu muhimman kayyakin da za a yi amfani da su wajen gudanar da zaɓukan 2023 su na nan lafiya ƙalau cikin tsaro. Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Mista Festus Okoye ne ya sanar da hakan a wani…
Read More
Al-Mustapha ya zargi ƙasashen Yamma da tsawaita ta’addancin Boko Haram

Al-Mustapha ya zargi ƙasashen Yamma da tsawaita ta’addancin Boko Haram

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Ɗan takarar Shugaban Nijeriya a Jam'iyyar ‘Action Alliance’ kuma tsohon jami’in tsaron tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji Marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi zargin cewar, akwai wata maƙarƙashiya da ƙasashen Yamma suke yi na tsawaita ta’addancin Boko Haram a ƙasar nan. Al-Mustapha ya yi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa kan zaɓen shekara ta 2023 da aka gudanar a makon da ya gabata a birnin Abuja. Ya ce duk da cewar, an ƙyanƙyashe ta’addancin Boko Haram ne a ranar 1 ga watan Nuwamba na shekarar 1999, amma an ƙudura aniyyar sa…
Read More