Labarai

DSS ta kama Tukur Mamu a filin jirgin saman Kano

DSS ta kama Tukur Mamu a filin jirgin saman Kano

Daga BASHIR ISAH Jami'an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama Malam Tukur Mamu a Bababban Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Jihar Kano. Tun farko Mnahaja ta rawaito yadda jami'an tsaro suka tsare Mamu a birnin Alƙahira, babban birnin ƙasar Masar, inda daga nan aka dawo da shi Nijeriya. Mamu ya ce shi da iyalansa suna kan hanyarsu ta zuwa Ƙasar Saudiyya ne inda aka tsare su na tsawon awa 24 a Alƙahira. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, jirgin da ya dawo da su Tukur Mamu ya sauka filin jirgin saman Kano ne da misalin ƙarfe…
Read More
An tsare Tukur Mamu da matansa a Masar

An tsare Tukur Mamu da matansa a Masar

Daga BASHIR ISAH An tsare mawallafin nan wanda ke shiga tsakani wajen kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasan hanyar Kaduna-Abuja da aka yi garkuwa da su, Tukur Mamu, a ƙasar Masar. An tsare Mamu ne a ranar Talata a Babban Filin Jirgin Saman Alƙahira a daidai lokacin da yake shirin tafiya Saudi Arebiya. Mamu, shi ne mawallafin jaridar nan ta Desert Herald, kuma mai magana da yawun fitaccen malamin Islaman nan na Kaduna, Ahmad Gumi, ya taka rawa wajen kuɓutar da wasu daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna a watan Maris da ya gabata. Sai…
Read More
Yajin aikin ASUU: Jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya suna ta samun ƙarin ɗalibai

Yajin aikin ASUU: Jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya suna ta samun ƙarin ɗalibai

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai jami'o'i masu zaman kansu a Nijeriya sun ƙara tumbatsa sakamakon ɗalibai da suke rigegeniyar shiga sakamakon rufe jami'o'in gwamnati da aka yi sanadiyyar yajin aikin ASUU. Idan za a iya tunawa, tun 14 ga watan Fabrairu, 2022 ne aka tsayar da duk wata hada-hada ta koyarwa ko koyo a jami'o'in Nijeriya mallakar gwamnati saboda yajin aikin da ƙungiyar Malamai da ma'aikatan jami'o'i (ASUU) suka tsunduma. Ƙungiyar tana neman kuɗaɗen inganta jami'o'in ne daga wajen gwamnati na yarjejeniyar 2009 FGN/ASUU da alawus-alawus na malaman da ya maƙale da kuma tabbatar da adalci a…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin harajin kiran waya

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin harajin kiran waya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙarin harajin kiran wayar sadarwa da ofishin kasafin kuɗi na Nijeriya ke ƙoƙarin yi. Gwamnatin ta dakatar da qarin kaso biyar cikin dari ne da ake shirin yi a baya. Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fasahar Zamani, Isa Ali Pantami ne ya sanar da dakatarwar a ranar Litinin yayin taron ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa na haraji kan hanyoyin sadarwa don bunqasa ɓangaren tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani a Abuja. Ministan ya ce tun tuni fannin sadarwa ya cika da harajai da yawa. Gwamnatin Tarayya ta…
Read More
Ruɗani yayin da zaɓen ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa ya samar da shugabanni biyu

Ruɗani yayin da zaɓen ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa ya samar da shugabanni biyu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An samu ruɗani yayin da babban zaɓen da Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS) ta gudanar ya fitar da ’yan takara daban-daban guda biyu a matsayin shugaban ƙungiyar ɗalibai. Wannan ruɗani dai ya sa rikici ya ɓarke tsakanin ɓangarorin ƙungiyar kare haƙƙin ɗaliban biyu. Sakamakon haka, ƙungiyar ta kira hira da manema labarai na gaggawa don sanar da al'umma halin da ake ciki. NANS wadda ita ce ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa ta Nijeriya da ke kare haƙƙin ɗalibai masu karatu a manyan jami'o'in Nijeriya da na ƙasashen waje an ba da rahoton kammala babban zaɓenta a ranar…
Read More
2023: Adamu ya nemi haɗin kan sarakunan gargajiya

2023: Adamu ya nemi haɗin kan sarakunan gargajiya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nemi goyon baya da haɗin kan sarakunan gargajiya don gudanar da babban zaɓen 2023 cikin nasara. Adamu ya buƙaci hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu-Bashar a Fadar Abdullahi Fodio da ke Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi. Shugaban APCn ya ziyarci Jihar Kebbi ne don halartar ɗaurin auren 'ya'yan Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa na APC, Alhaji Suleiman Muhammad-Argungu. Da yake jawabi a fadar Sarkin, Adamu ya ce, "Bikin aure ne ya kawo mu Kebbi, inda muka ga dacewar mu kawo gaisuwar…
Read More
Buba Marwa ya tallafa wa matasan Ƙaramar Hukumar Fage da kekunan ɗinki

Buba Marwa ya tallafa wa matasan Ƙaramar Hukumar Fage da kekunan ɗinki

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Shugaban Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi na Ƙasa, Buba Marwa ya bayar da tallafin kekunan ɗinki guda 50 da kuɗi Naira 1,000,000 don dogaro da kai ga matasan Ƙaramar Hukumar Fagge. Tallafin wanda shugabar hukumar NDLEA mai kula da Jihar Kano da Jigawa Hajiya Maryam Sani ta miƙa a madadin shugaban a taron da aka gudanar a safiyar Alhamis a sakatariyar ƙaramar hukumar cikon alkawarin da ya yi ne ga matasan a yayin da ya kai ziyarar aiki yankin a 2019 na cewa zai bada kekunan ɗinki guda 100 da Naira 2,000,000. Cikin alƙawarin…
Read More
Gurɓacewar tarbiyyar ɗalibai ya sa gwamnatin Bauchi rarrabe makarantun maza da na mata – Kwamishina

Gurɓacewar tarbiyyar ɗalibai ya sa gwamnatin Bauchi rarrabe makarantun maza da na mata – Kwamishina

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta bayyana aniyarta na rarrabe makarantun ɗalibai maza da na mata, la’akari da yadda gurɓacewar tarbiyya ta kasance ruwan dare a tsakanin makarantun ta na sakandare a ɗaukacin cikin jihar. Kwamishina mai lura da lamuran ma’aikatar, Dokta Aliyu Usman Tilde da yake bayyana wannan aniya ta gwamnati a garin Bauchi jiya Alhamis, ya nuna matuƙar damuwar gwamnatin jiha bisa yadda tarbiyyar ɗalibai a makarantunta ya kasance abin kaico. Dokta Aliyu Tilde ya bayyana cewar, “wannan shiri na makarantun mata zalla da na maza zalla tsohon shiri ne da a yanzu…
Read More
Bayan shekaru 15, Tiwita ta samar da tsarin gyara rubutu bayan wallafawa

Bayan shekaru 15, Tiwita ta samar da tsarin gyara rubutu bayan wallafawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dandalin sada zumunta na Tiwita, a ƙarshe, ya fitar da fasalin da aka daɗe ana nema na damar yin canje-canje ga rubutu bayan an wallafa, wato 'Edit Tweet'. Kamfanin a ranar Alhamis, 1 ga Agusta, 2022, ya bayyana cewa, wasu masu amfani za su iya fara ganin fasalin gyaran rubutun a cikin manhajarsu saboda daman an daɗe a jiran hakan. A cewar Tuwita, fasalin a halin yanzu yana fuskantar ‘gwajin ciki’. “Ma'aikatan ciki neza su fara amfani da sabon fasalin na 'Edit Tweet', sannan kuma a faɗaɗa shi zuwa ga yawan masu biyan kuɗi na ‘Twitter…
Read More
Buhari ya miƙa ragamar buga kuɗin Nijeriya ga ɗan uwan matarsa

Buhari ya miƙa ragamar buga kuɗin Nijeriya ga ɗan uwan matarsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani rahoto daga jaridun Nijeriya ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin Ahmed Halilu matsayin sabon manajan daraktan Nigerian Security Printing and Minting Company, NSPMC.  Amintar shugaban ƙasan kan naɗin Halilu matsayin manajan daraktan kamfanin buga kuɗin na Nijeriya ya biyo bayan shawarar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele. Wannan naɗin ya zo ne bayan watanni kaɗan da murabus ɗin Abbas Masanawa, tsohon manajan daraktan NSPMC.  Sai dai, naɗin da aka yi wa Halilu zai aiki ne matsayin muƙaddashin manajan daraktan bayan shawara ta musamman da Godwin Emefiele, gwamnan babban…
Read More