23
Aug
Wata mata ta kashe mijin abokiyar maɗigonta ta hanyar daɓa masa wuƙa a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Rahotanni sun nuna cewa, ba a bayyana sunan matar da ta yi kashe Ikechukwu Onuma da aka fi sani da ‘Ayaaya Onye-Obodo’ ba, amma tana aiki a Kwalejin horo na lafiya a Onitsha. Ta gudanar da wannan aika-aikar ne a gidan mutumin a kan titin Ogboli da misalin qarfe 9:20pm na daren Talata a birnin Onitsha da ke jihar Anambra. Marigayi Mista Onuma ya isa gida ba tare da matarsa ta sani ba, inda ya tarar da ita da…