19
Aug
Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabin ta Ƙasa (NBC) ta ba da sanarwar rufe wasu tashoshin rediyo da talabijin a faɗin Nijeriya. Darakta Janar na hukumar, Balarabe Shehu ne ya ba da sanarwar rufe tashoshin, yana mai cewa an ɗauki matakin haka ne saboda ƙin sabunta lasisinsu da tashoshin suka yi. Shehu ya bai wa rassan hukumar a jihohi umarni kan su haɗa kai da hukumomin tsaro wajen tabbatar da kafofin da lamarin ya shafa sun daina aiki cikin sa'o'i 24 masu zuwa. Ya ƙara da cewa, gwamnati na bin tashoshin da abin ya shafa bashin…