13
Jul
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Nijeriya na daga cikin ƙasashen duniya na sahun farko da jama'ar ƙasar ta ke da son addini. Wata majiyar ma na cewa, Nijeriya ce ƙasar da mutanen ta ke da tsananin son al'amarin addini. Komai na 'yan Nijeriya sai ka samu addini a ciki, ko da kuwa a sautin ƙarar waya ne, sai ka fahimci ƙarar wayar Musulmi da ta wanda ba Musulmi ba. Muna nuna son junan mu saboda addini, mu taimaki bare saboda addini, mu gujewa ɗan uwa saboda addini. Akwai masu addini na tsakani da Allah, akwai 'yan na gada, 'yan son zuciya…