29
Jan
Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyarta ta kyautata rayuwar talakawa da marasa galihu a fadin kasa inda ta raba wa mata su 8,000 tallafin kudi na naira 20,000 ga kowaccensu a karkashin shirin nan nata na tallafa wa matan karkara da kudade. Ministar Jinkai da Agaji, Sadiya Umar Farouq ce ta bada jaddadin yayin kaddamar da shirin tallafa wa matan a Legas. Da take jawabi a wajen taron kaddamar da shirin a bisa wakilcin babban sakataren ma'aikatarta Bashir Nura Alkali, Sadiya ta ce, "Kudirinmu shi ne mu ga mata sama da 8,000 sun amfana da shirin a tsakanin…