22
May
Daga UMAR M. GOMBE Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya ce abin kaɗuwa ne ainun rasuwar da Babban Hafsan sojoji na 21, Lt General Ibrahim Attahiru, ya yi a haɗarin jirgin sama kimanin watanni huɗu da naɗa shi kan sabon muƙaminsa. Cikin saƙon ta'aziyyar da ya miƙa, Janar Magashi ya ce haɗarin jirgin wanda ya yi ajalin Attahiru da sauran jami'an da suke tare, babban ibtila'i ne ga ƙasa. Ministan ya miƙa ta'aziyyarsa ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Rundunar Sojoji da iyalan mamatan da ma ƙasa baki ɗaya dangane da wannan babban rashi da ya auku. Magashi…