Month: May 2021

Hajjin 2021: Kano ta ƙaddamar da shirin wayar da kan maniyyata

Hajjin 2021: Kano ta ƙaddamar da shirin wayar da kan maniyyata

Daga AISHA ASAS Hukumar Kula da Walwalar Maniyyata ta Jihar Kano, ta ce ta soma gudanar da shirin wayar da kan maniyyatan jihar a matsayin wani mataki na shirye-shiryen hajjin bana. Sakataren Hukumar, Alhaji Mohammed Abba Danbatta, ya bayyana wa manema labarai a Kano a cewa, shirin wanda aka ƙaddamar da shi a ranar Asabar da ta gabata zai ci gaba da gudana a cibiyoyin yin rajistar hajjin da ake da su a jihar. Ya ce manufar shirin shi ne wayar da kan maniyyatan jihar da kuma ilmantar da su kan tsare-tsaren hanjjin bana da kuma yadda ya kamata su…
Read More
‘Yan bindiga sun sace matar shugaban matasan APC a Oyo

‘Yan bindiga sun sace matar shugaban matasan APC a Oyo

Daga WAKILINMU Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne, sun sace matar shugaban matasa (youth leader) na jam'iyyar APC a jihar Oyo a yammacin Lahadin da ta gabata. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna an sace matar Dr Adenike Oni-Salawu ne a gaban gidansu da ke yankin hanyar tsohuwar Ife a Ibadan. A daidai lokacin da matar ta sauka a motarta sannan take ƙoƙarin buɗe get don ta shige gida sai 'yan bindigar suka yi amfani da wannan dama suka far mata ɗauke da muggan makamai tare da yin awon gaba da ita. Wata majiya ta kusa da shugaban…
Read More
Dalilin da ya sa Buhari bai halarci jana’izar attahiru ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Dalilin da ya sa Buhari bai halarci jana’izar attahiru ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari ya bayyana dalilin da ya sa bai samu halartar wurin jana'izar tsohon Shugaban Rundunar Sojoji, Lt. Gen. Ibrahim Attahiru tare da wasu jami'ai 10 da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata. Attahiru da sauran jami'ai goma sun cim ma ajali ne a haɗarin jirgin saman da ya rutsa da su a Juma'ar da ta gabata a Kaduna. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Shugaba Buhari na buƙatar bayanan tsaro na aƙalla sa'o'i 48 kafin ya ba fadarsa don halartar kowane irin taro. Da alama dai rashin ganin Buhari a wajen taron…
Read More
An soma bincike kan haɗarin jirgin da ya ci ran Attahiru a Kaduna – Cibiya

An soma bincike kan haɗarin jirgin da ya ci ran Attahiru a Kaduna – Cibiya

Daga AISHA ASAS Cibiyar Binciken Haɗurra a Nijeriya (AIB-N) ta soma gudanar da bincike kan haɗarin jirgin saman da ya auku a Kaduna a Juma'ar da ta gabata wanda ya yi sanadiyar mutuwar Babban Hafsan Hafsoshi, Ibrahim Attahiru tare da wasu jami'ai. Babban Manajan Sashen Hulɗa da Jama'a na Cibiyar, Tunji Oketunbi, shi ne ya bayyana hakan a wani bayani da ya fitar a Legas a Asabar da ta gabata. Oketunbi ya ce tuni cibiyar ta sunkuya bincike don gano musabbabin aukuwar haɗarin wanda a cewarsa har ma an kai ga gano wasu muhimman na'urori a inda jirgin ya rikito…
Read More
Saƙon ta’aziyya: Buratai ya jinjina wa Attahiru

Saƙon ta’aziyya: Buratai ya jinjina wa Attahiru

Daga UMAR M. GOMBE Tsohon Babban Hafsan Hafsoshi, Ambasada Tukur Buratai (Lt Gen Rtd) ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da samun labarin rasuwar magajinsa, Lieutenant General Ibrahim Attahiru, da sauran jami'an da haɗarin jirgin sama ya rutsa da su a ranar 21, Mayu, 2021 a garin Kaduna. Buratai ya bayyana kaɗuwar tasa ne a saƙon ta'aziyya da ya miƙa, tare yin amfani da wannan dama a madadinsa da iyalansa wajen miƙa ta'aziyyarsa dangane da wannan babban rashi ga Shugaban Ƙasa da iyalan marigayan, Ministan Tsaro, Shugaban Rundunanr Sojijin Sama ta Nijeriya da ma Nijeriya baki ɗaya. Ya ce wannan…
Read More
Bayan Azahar za a yi jana’izar Attahiru

Bayan Azahar za a yi jana’izar Attahiru

Daga AISHA ASAS Kawo yanzu, jama'a da dama na tsumayar jana'izar Babban Hafsan Sojoji, Ibrahim Attahiru, wanda za a gudanar a babban Masallacin Abuja. Manyan jami'an soja 6 ne za a yi wa Sallar Jana'izar waɗanda suka rasu sakamakon hadarin jirgin sama da ya rutsa da su a Kaduna. Yayin da ragowan sojojin za a binne su ne daidai da tsarin addininsu na Kirista.
Read More