19
Jul
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sake tsanantar rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ya sake jefa kasuwar ɗanyen mai ta duniya cikin ruɗani, yayin da farashin mai ya yi tashin gwauron zabo sakamakon fargabar katsewar samar da mai, yiwuwar ƙarin takunkumi da kuma barazanar tsaro a mashigar ruwan Hormuz, wadda ke daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai a duniya. A daidai wannan lokaci ne kuma Matatar Mai ta Dangote ta sanar da sauya tsarin sayar da kayayyakinta, inda ta dakatar da karɓar kuɗin naira tare da fara sanya farashin man fetur (PMS), dizal da man jiragen sama (ATK) da dalar…
