Kasashen Waje

Ana cigaba da farfaɗo da yankin Xinjiang bayan cimma burin kawar da talauci

Ana cigaba da farfaɗo da yankin Xinjiang bayan cimma burin kawar da talauci

Daga CMG HAUSA An labarta yayin taron watsa labarai game da “Sakamakon da yankin Xinjiang na ƙasar Sin ya samu cikin shekaru goma da suka gabata” a safiyar yau Asabar cewa, gwamnatin yankin Xinjiang tana kara mai da hankali kan aikin da take gudanarwa a ƙauyuka bayan da aka cimma burin kawar da talauci, kuma nan gaba za ta ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da kauyukan yankin daga fannoni biyar wato sana’o’in ƙauyuka, da ƙwararru, da al’adu, da hallitu masu rai da marasa rai da kuma ƙungiyoyin JKS, ta yadda za a cimma burin farfaɗo da ƙauyukan dake faɗin yankin.…
Read More
Xi ya amsa wasiƙar iyalan fursunonin sojojin Birtaniya na jirgin ruwa samfurin “Lisbon Maru”

Xi ya amsa wasiƙar iyalan fursunonin sojojin Birtaniya na jirgin ruwa samfurin “Lisbon Maru”

Daga CMG HAUSA A kwanakin baya shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya amsa wasiƙar da iyalan fursunonin sojojin Birtaniya da aka kama a jirgin ruwan dakon kaya na “Lisbon Maru” na ƙasar Japan suka aika masa, inda ya bayyana cewa, yana fatan ƙarin abokan Sinawa na Birtaniya, za su ba da gudumowa ga hulɗar dake tsakanin Sin da Birtaniya. Xi ya bayyana cewa, masuntan tsibirin Zhoushan dake lardin Zhejiang na ƙasar Sin sun ceto fursunonin sojojin Birtaniya da suka faɗa cikin teku daga jirgin ruwan “Lisbon Maru” sakamakon harbin sojojin Amurka, a shekarar 1942, lamarin da ya nuna cewa, ƙasar Sin da…
Read More
Za a sanya harshen Sinanci cikin manhajar ilimi a Ghana

Za a sanya harshen Sinanci cikin manhajar ilimi a Ghana

Daga CMG HAUSA Babban daraktan ma’aikatar ilimi ta ƙasar Ghana, Divine Yao Ayidzoe, ya ce nan bada jimawa ba, za sanya Sinanci cikin manhajar ilimi ta ƙasar. Daraktan ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin wani taron da aka shiriya jiya a cibiyar nazarin harshen Sinanci ta Confiscius dake jami’ar Cape Coast ta Cape Coast, babban birnin yankin tsakiyar Ghana. Da yake jadadda ƙaruwar muhimmancin koyon harshen Sinanci, baya ga harshen da ƙasar ke amfani da shi a hukumance, daraktan ya ce bisa la’akari da faɗaɗar tattalin arzikin ƙasar Sin zuwa na biyu mafi girma a duniya, haƙiƙa…
Read More
Ƙwararru: Shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” na bunƙasa ci gaban nahiyar Afirka

Ƙwararru: Shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” na bunƙasa ci gaban nahiyar Afirka

Daga CMG HAUSA Wasu masu bincike, kuma ƙwararru game da al’amuran ƙasa da kasa na yankin gabashin Afirka, sun bayyana shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” da ƙasar Sin ta gabatar, a matsayin manufar dake ingiza ci gaban nahiyar Afirka. Ƙwararrun sun yi tsokacin ne a jiya Laraba, yayin taron yini guda da ya gudana ta kafar bidiyo, mai taken "Muhimmancin shawarar ziri ɗaya da hanya daya ga nahiyar Afirka." Ɗaya daga cikin ƙwararrun Frederick Golooba Mutebi daga ƙasar Uganda, ya ce shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya, ta zamo ginshikin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, da rage matsalar…
Read More
Duniya ba ta buƙatar duk wani nau’i na yaƙin cacar baka

Duniya ba ta buƙatar duk wani nau’i na yaƙin cacar baka

Daga SAMINU HASSAN A baya bayan nan, yayin zaman kwamitin tsaro na MƊD game da rikicin ƙasar Ukraine, an tabo muhimman batutuwa game da halin da ake ciki, don gane da wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa, wanda a yanzu haka ya doshi wata na 7. Tuni sassan duniya daban daban suka dandani raɗaɗin tasirin wannan rikici, kama daga kamfa, da hauhawar farashin makamashi a sassan nahiyar Turai, zuwa ƙarancin hatsi, da takin zamani da sassan ƙasashe masu tasowa, kamar nahiyar Afirka ke fama da shi. Game da wannan batu, tsagin ƙasar Sin na ganin a wannan…
Read More
Xi ya aike da wasiƙar taya murna ga taron haɗin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka karo na biyar

Xi ya aike da wasiƙar taya murna ga taron haɗin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka karo na biyar

Daga CMG HAUSA Yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasiƙar taya murna ga taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka karo na 5. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tun bayan kafa shi shekaru 10 da suka gabata, dandalin ya samar da wata muhimmiyar kafa ga kafofin watsa labaru na Sin da Afirka, wajen inganta tattaunawa da haɗin gwiwa, kana ya taka muhimmiyar rawa wajen sa ƙaimi ga yin musaya da yin koyi da juna, tsakanin wayewar kan Sin da Afirka, da zurfafa cikakkiyar dangantakar haɗin gwiwa bisa manyan tsare-tsare…
Read More
Jarin Sin ya taimaka wajen raya tsarin samar da kayayyaki a Afrika

Jarin Sin ya taimaka wajen raya tsarin samar da kayayyaki a Afrika

Daga CMG HAUSA Majalisar kula da harkokin kasuwanci tsakanin Sin da Afrika (CABC), ta fitar da wani sabon rahoto kan jarin da ƙasar Sin ta zuba a ƙasashen Afrika, wanda ya bayyana cewa, cikin shekaru 22 da suka gabata, ɓangarorin biyu sun samu dimbin nasarori ta kowacce fuska tare da haɗa gwiwa a bangarori da dama. Rahoton da aka fitar a jiya, ya ce manyan jami’an majalisar sun ce kamfanonin ƙasar Sin sun yi kyakkyawan tasiri, kana sun kasance wani ɓangare mai matuƙar amfani na kasuwar Afrika. Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa
Read More
Yaƙin Afghanistan ba fim ba ne

Yaƙin Afghanistan ba fim ba ne

Daga CMG HAUSA “Dana ɗaya ya faɗo daga jirgin sama a filin jiragen sama na Kabul, ɗayan kuma har yanzu ba mu san inda yake ba”. Kalaman da Mohammad Rezayee, dan ƙasar Afghanistan ya yi a kwanan baya a yayin da yake tattaunawa tare da jaridar The Times ta Burtaniya a kwanan baya, sun tunatar da mu kan abin da ya faru a shekara ɗaya da ta gabata. A watan Agustan shekarar 2021, Amurka ta janye sojojinta daga ƙasar Afghanistan ba tare da ɗaukar nauyin da ke bisa wuyanta ba, matakin da ya sa dubu dubantar ‘yan Afghanistan suka kutsa…
Read More
Sai an sha wuya a kan sha daɗi

Sai an sha wuya a kan sha daɗi

Daga IBRAHIM YAYA Sanin kowa ne cewa, duk ƙasar dake fatan samun ci gaba har ma a rika jin amonta a duniya, wajibi ne al’ummarta su zage damtse wajen ganin wannan buri ya tabbata. Kamar sauran al’ummomin ƙasashen duniya, al’ummar Sinawa sun hada ƙarfi da ƙarfe wajen gina ƙasar Sin mai bin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta ƙasar Sin a sabon zamani. Gagarumin ci gaban da ƙasar Sin ta cimma a cikin shekaru 10 da suka gabata (2012-2022), sun haɗa da fannonin tattalin arziki, da binciken sararin samaniya, da fannin ƙirƙire-ƙirƙire da inganta muhalli da zaman rayuwar jama’a da…
Read More
Kyan alƙawari cikawa

Kyan alƙawari cikawa

Daga CMG HAUSA Akwai wasu mutane 2, ɗaya ya iya magana sosai, amma yakan manta da maganar da ya faɗa, yayin da ɗayan ba ya son magana, sai dai duk wani alƙawari da ya yi, zai yi ƙoƙarin cika shi. A cikin mutanen nan 2 wanne ka fi so? Tabbas za a ƙulla abota tare da mutum na biyu ko? Saboda “Alƙawari kaya ne”. Ba za a iya dogaro kan wani ba, idan ba zai iya cika alƙawari ba. Wani babban dalilin da ya sa ƙasar Sin ta zama aminiyar ƙasashen Afirka, shi ne yadda suke iya dogaro da ita,…
Read More