27
Aug
Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A ƙarshe dai kamar yadda kowa ya gani a labaru shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da ministocin sa 45 da Majalisar Dattawa ta tantance gabanin ta tafi hutu. In za a tuna har ma wataƙila daɗin kammala aikin tantancewar ya sa shugaban majalisar Godwill Akpabio ya ce ya tura ihsani ga dukkanin ’yan majalisar ɗari da tara don su more hutun. A wani yanayi da a ka fahimci an ja hankalin Akpabio cewa ya na jawabi ne kai tsaye da a ke yaɗawa ta kafar talabijin, sai ya waske ko ya gyara zance…