Ra’ayi

Shin shugaba Bazoum zai koma karaga?

Shin shugaba Bazoum zai koma karaga?

Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Idan mu ka shiga nazarin yadda lamura su ke a jamhuriyar Nijar za mu gane sojojin nan ba su da niyyar sauka daga mulki don dawo da gwamnatin dimokraɗiyya ta shugaba Muhammad Bazoum. Kazalika amfani da karfin soja na bukatar gwanaye da za su iya yin hakan ta yaƙi da dabarun kifar da jutin mulki ba yaƙi da ƙasar Nijar ba. Kafin ma na yi nisa zan ce a wajen Allah Maɗaukakin Sarki mai ba da mulki wannan abu ne mai sauƙi. Mu duba misalin yadda a ka kare dimokraɗiyya a Gambia bayan da tsohon…
Read More
Kawar da bautar da ƙananan yara

Kawar da bautar da ƙananan yara

Akwai wani al'amari mai matuƙar tayar da hankali da ban tausayi kan yadda ake amfani da yara masu ƙananan shekaru maza da mata don yin aiki ko bauta a gidaje da sauran wurare da suka haɗa da shaguna, otel-otel, wuraren kwana na manyan makarantu ko ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’o’i. Akasarin yaran ’yan ƙasa da shekaru 15 ne kuma ana ɗaukarsu ne da nufin yin aikace-aikacen da suka haɗa da shara, wanke-wanke, wanki, goge-goge, ɗebo ruwa da rainon jarirai da kula da yayayyun yara da makamantansu. Mafi yawan yaran ana kawo su cikin birni daga ƙauyuka lokaci zuwa lokaci, ta…
Read More
Juyin mulki a Nijar ya tono gara daga rami

Juyin mulki a Nijar ya tono gara daga rami

Tare Da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wata sabuwar fitina da ke ƙoƙarin kunno kai a Afirka, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a ranar 26 ga watan Yuni, shi ne tasirin yaƙin cacar baka tsakanin Rasha da Amurka, sakamakon yaƙin Ukraine da Rasha da manyan ƙasashen duniya suke hassalawa. Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ya kira wani taron gaggawa inda suka tattauna kan yadda za a ɓullowa wannan juyin mulki da ke neman durƙusar da mulkin Dimukraɗiyya a yankin. Daga cikin ƙudirorin da taron…
Read More
Zubar da jini a Arewa: Ya kamata mu farka!

Zubar da jini a Arewa: Ya kamata mu farka!

Abin da ya ke faruwa a kasar nan har wasu su ke daukarsa tamkar wasa, ko abin nishaɗin da za a zauna a bakin layi a tattauna cikin raha, ko da rabin kwatankwacinsa ya ke faruwa a wata ƙasar wacce ke da cikakkun mutane masu hankali da sanin ciwon kai, da wuya su yarda a kai wani lokaci ba su sauke duk wani shugaba da ke da hannu ko sakaci a cikin abin ba. A yanzu haka mutanen da ke kallon labaran halin da muke ciki suna nan suna mamakin ko mu waɗanne irin mutane ne? Ta yaya za a…
Read More
Saƙo ga Musulmai daga Tiktok

Saƙo ga Musulmai daga Tiktok

Na yi dogon rubutu na kammala a kan wannan bidiyo, amma sai na neme shi na rasa. Dole sai da na sake komawa tiktok na nemo bidiyo ɗin. Ina ganin wannan bidiyo na ƙasa yana ishara ne da hadisin da aka ce Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) ya faxa ne, da yake cewa "…Dan Allah ku kula da mata". A fahimtata ya danka su amana ne a hannunmu, amma ko shakka babu, wannan amana ta mata da 'ya'ya da aka damqa mana, ta tabbata da yawa daga cikinmu mun ci wannan amana. Da farko dai, a jiya da dare…
Read More
Shigar Nijeriya hidimar yaƙi a Nijar: A yi hattara ko a sha kunya

Shigar Nijeriya hidimar yaƙi a Nijar: A yi hattara ko a sha kunya

Bayanan da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke Yi da Nijeriya da ECOWAS na shirin kai hari wa sojojin Nijar, babbar kasada ce kowa ya iya allonsa ya wanke su ji da matsalar Zamfara da matsalar yunwa da boren da talakawa ke shirin shiga. Sun fi kowa sanin ba a raina yaƙi su tambayi Rasha a Ukraine yadda wanki ya Kai su dare kowane gefe ke asarar soja da dukiya. Sojojin Nijar ba kanwar lasa bane idan suka yi wannan kuskure kafin su kai Maradi ko Tahwa kan hanyar zuwa Niamey karon ba zai musu daɗi ba. Saboda na shiga Nijar…
Read More
Malagi ya zamo minista

Malagi ya zamo minista

An ce mai haƙuri ya kan dafa dutse har ya sha roman sa. Ga dukkan alamu gwamnati shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu GCFR ta na son kafa kyakkyawan tarihi na gina gwamnati da kwararru ta fuskoki da dama. Jihar Neja za ta yi ministoci maau kwarewa kuma fitattu ta fuskar gogewa domin ɗauko Muhammed Idris Malagi a yi masa minista, wanda hakan wata manuniya ce a kan yadda shugaba Tinubu ke da tunani da ƙoƙarin janyo duk wanda ya cen centa. Ba zan ida wannan rubutu ba har sai na yaba ma ɗauko mutane kamar Act Musa Dangiwa da Hannatu…
Read More
Shin lauyoyi ne kaɗai su ka yi fushi da sake kama Emefile?

Shin lauyoyi ne kaɗai su ka yi fushi da sake kama Emefile?

Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Zan fara da batun Godwin Emefiele kafin shiga batun tsadar rayuwa. Haƙiƙa a ’yan kwanaki biyun nan labarun yadda ta kaya a kotun Legas kan dakataccen gwamnan babbban banki Godwin Emefiele ya zama kan gaba a kafafe. Ba kotu kaɗai ce ta buƙaci ko umurci ’yan sandan farin kaya DSS ssu sake Emefiele ko su gurfanar da shi gaban kotu. DSS ta cimma umurnin kotun don maimakon ta sake Emefiele ta zaɓi gurfanar da shi gaban kotu ne don fara cajin da da dalilan kama shi fiye da wata ɗaya da ya wuce. Rundunar farin…
Read More
Daƙile matsalar mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya

Daƙile matsalar mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya

Matsalar mace-macen mata da yara a lokacin ciki ko haihuwa dai ta jima ta na ci wa ƙasashe masu tasowa tuwo a ƙwarya. Alal misali, ƙasashen da suka ci gaba mata 7 zuwa 15 ne ke mutuwa a cikin mata masu juna 100,000 daga lalurar ciki ko haihuwa; amma a ƙasashe masu tasowa har wajen mata 100-300 ne kan rasu sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa. Wani sabon rahoton da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya suka fitar na cewa a duk minti biyu mace na mutuwa a duniya yayin da take ɗauke da juna biyu ko haihuwa. Hakan na ƙara nuna rashin…
Read More
Makamashi: Albarkatun ƙasa a Nijeriya

Makamashi: Albarkatun ƙasa a Nijeriya

Tare Da BASHIIR MUDI YAKASAI Allah Maɗaukakin Sarki ya albarkanci wannan ƙasa ta Nijeriya da albarkatun ƙarƙashin ƙasa, da kusan babu wata a afrika da zata yi gogayya da ita. Kasace da zata taka kowacce irinn rawa a kasuwar duniya a fannin albarkatun ƙarƙashin ƙasa kamar Azurfa da tagulla da tama da kuza da zinariya da lu’u-lu’u da kuma uwa- uba ɗanyan man fetur da gas da kuma dangoginsa. Tun bayan yaƙin duniya na biyu, ƙasar Birtaniya uwar gijiyar wannan ƙasa ta Nijeriya take kwasar wannan garabasar a gurare daban-daban, kamar tama da kuza a yankin Jos a jahar filato…
Read More