29
Mar
Daga UMAR M. GOMBE An kammala Musabaƙar Karatun Ƙur'ani ta Ƙasa karo na 35 a Kano tare da Muhammad Auwal Gusau daga jihar Zamfara a matsayin wanda ya zama gwarzo a ɓangare maza, yayin da Nusaiba Shu’aibu Ahmed daga Kano, ta zama gwarzuwa a ɓangaren mata. Albarkacin bajintar da suka nuna a yayin gasar ya sa Gwamnatin Kano ta yi wa jaruman biyu kyautar kuɗi ta Naira milyan N2.5 ga kowannensu. Da yake jawabi a wajen rufe gasar Asabar da ta gabata, Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, a bisa wakilicin mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce maza…