26
Mar
Wani rahoton musamman da jaridar Blueprint ta buga a ranar Talata ta makon jiya ya nuna cewa a cikin watanni uku kacal ’yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare a makarantu aƙalla guda biyar a yankunan Arewa-maso-yamma da Arewa-maso-gabas. Hakan ya haifar da damuwa a kan batun samar da ilimi ba kawai a waɗannan yankunan kaɗai ba har ma da lardin Arewa baki ɗayan sa. Rahoton ya ambaci jihohin Katsina, Zamfara da Kaduna a Arewa-maso-yamma da kuma Neja a Arewa-ta-tsakiya a matsayin inda ayyukan ta’addancin ’yan bindigar ya fi ta’azzara. Hari na baya-bayan nan da aka kai, an kai…