25
Mar
Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya musunta zargin da ake yaɗawa kan cewa ruwa ya yi tsami tsakaninsa da tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu. Buhari ya musunta zargin hakan ne ta wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar inda ya bayyana cewa hakan ba gaskiya ba ne. Sanarwar ta nuna cewa, hasali ma alaƙar da ke tsakanin dattawan biyi sai armashi da ƙarƙo take ƙarawa. A cewar Shehu Garba, “Fadar Shugaban Ƙasa na faɗa da babbar murya cewa babu wani rashin jituwa a tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari…