19
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Farashin kayayyaki ya hauhawa a watan Maris da ya gabata zuwa kashi 24.23 cikin 100 a sababbin alƙaluman da aka koma amfani da su a Nijeriya. Rahoton da hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta fitar a ranar Talata ya nuna cewa an samu ƙarin hauhawar farashin da kashi 1.05 idan aka kwatanta da watan Fabrairu na 2024 daga 23.18 da aka samu a watan. Wannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin a Nijeriya tun bayan da hukumar National Bureau of Statistics (NBS) ta sauya ma'aunin da take amfani da shi wajen fitar…