20
Aug
Daga CMG HAUSA A safiyar yau ne, ƙasar Sin ta yi amfani da rokar Long March-2D wajen harba rukunin taurorin dan Adam zuwa sararin samaniya, wanda ya nuna nasarar da ƙasar ta cimma wajen amfani da rokar wajen harba kumbuna sau 103 a jere. Nasarorin da aka cimma a baya wajen amfani da rokar ta Long March a jere shi ne 102, wanda aka fara cimmawa daga shekara 1996 zuwa ta 2011. Tun daga ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2020, rukunin rokar Long March na ƙasar Sin, ya cimma nasarori 103 a jere a cikin watanni 27 kacal, inda…