22
Nov
Daga WAKILINMU Wata mata da kawo yanzu babu wani cikakken bayani a kanta ta bayyana cewa tana amfani da jini mai ɗauke da ƙwayoyin cutar ƙanjamau wajen haɗa zoɓon da ta ke sayar wa jama’a. Matar wadda ta yi wannan ikirari ta bayyana hakan a yayin wani shiri mai taken ‘hada-hadar kasuwanci’ na MarketRunz da gidan rediyon Wazobia FM ya saba watsawa a duk daren ranar Laraba. A cikin shirin dai masu sauraro kan kira ta lambar waya su faɗi ababen da suke aikatawa a bayan fage kan harkokinsu na kasuwanci waɗanda abokan hulɗarsu ba su da masaniya a kai,…