24
Nov
Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Don ganin an rage yawan mutuwa a sanadiyar hatsari, Kamfanin Dexa da suke yi maganin nan na Boska ya raba wa mahaya babura sama da 600 hular kwano kyauta a Gombe. Kamfanin na Boska ya yi haɗin gwiwa ne da hukumar kiyaye hatsura ta ƙasa FRSC reshen Jihar Gombe don ganin cewa suna da ruwa da tsaki wajen faɗakar da masu baburan muhimmancin sanya hular kwano ga duk mai hawa babur. Da ya ke jawabi a lokacin raba hular kwanon Kwamishinan Ma’aikatar tsaron cikin gida na jihar Gombe Laftanal Abdullahi Bello mai ritaya, ya…