23
Feb
*Falasɗinu ta yi maraba da taron AU Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugabannin ƙasashen Africa sun yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke ƙaddamarwa kan yankin Gaza da sunan kare kai, yayin da suka buƙaci ƙasar ta dakatar da varin wutar ba tare da vata lokaci ba. Moussa Faki Mahamat, shugaban majalisar gudanarwar ƙungiyar ta AU ya ce wannan luguden wuta, babu abinda ke cikinsa illa cin zali da cin zarafi, kuma lokaci ya yi da duniya za ta mayar da Isra’ila cikin hayyacin ta. Kalaman na Faki na zuwa ne bayan doguwar maƙala da Prime ministan Falasɗinu…