Kasashen Waje

Ofishin jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ya yi Allah-wadai da kisan da Isara’ila ke yi wa Falasɗinawa

Ofishin jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ya yi Allah-wadai da kisan da Isara’ila ke yi wa Falasɗinawa

*Ya nuna alhini kan sace ɗaliba a arewacin Nijeriya Daga BASHIR ISAH Ofishin Jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ƙarƙashin Abdullah M. Abu Shawesh, ya tir da irin kisan kiyashin da Isra'ila ke yi wa Falasɗinawa. Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, ofishin ya fara bayani ne da nuna alhininsa kan ɗaliban da aka sace da sauransu a yankin Arewa. Abdullah M. Abu Shawesh ya ce, "Jin irin wannan labari yana motsa ni sosai kuma yana ƙara baƙin cikina "A cewar dokar Yahudawa, dole ne a kashe dukkan mazauna Gaza." "Hukumomin Isra'ila sun amince da wannan nau'in tunzura jama'a, kuma…
Read More
Firaministan Haiti ya kama hanyar murabus saboda matsin lambar ‘yan daba

Firaministan Haiti ya kama hanyar murabus saboda matsin lambar ‘yan daba

Firaministan Haiti Ariel Henry ya yada ƙwallon mangoro domin hutawa da ƙuda, wajen miƙa murabus ɗinsa a matsayin shugaban ƙasar da ke yankin Caribbean, bayan cimma matsaya da ƙungiyar ƙasashen yankin a matsayin mafita na warware rikicin siysar ƙasar. Shugaban ƙungiyar ƙasashen yankin Caribbean kuma shugaban ƙasar Guyana Irfaan Ali, wanda ya tabbatar da shirin murabus din Henry, ya yaba da matakin da ya kira wata dama ta kafa kwamitin shugaban ƙasa na riqon ƙwarya wanda zai naɗa firaministan riƙon kwarya. Henry mai shekaru 74 wanda ke riƙe da kujerar firanministan Haiti da ba zaɓen sa aka yi ba tun…
Read More
Birtaniya ta haramta wa likitoci ‘yan Nijeriya masu aiki a ƙasar zuwa da ‘yan uwansu

Birtaniya ta haramta wa likitoci ‘yan Nijeriya masu aiki a ƙasar zuwa da ‘yan uwansu

Daga BASHIR ISAH Ƙasar Birtaniya ta haramta wa ma’aikatan kiwon lafiya a ƙasar zuwa da 'yan uwansu ƙasar. Ofishin cikin gida na Birtaniya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne a matsayin ɓangare na ƙoƙarin da Gwamnatin ƙasar ke yi wajen yaƙi da matsalar shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba. Ta ƙara da cewa a bara kaɗai, jimillar ma'aikata 120,000 ne suka raka ma'aikata 100,000 zuwa Birtaniya. "Masu ba da kulawa a Ingila da ke aiki a matsayin masu tallafawa bakin haure kuwa, za a…
Read More
An ga watan Ramadan a Saudiyya

An ga watan Ramadan a Saudiyya

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙolin Saudiyya ta ce gobe Litinin shi ne zai zama 1 ga watan Ramadan na 1445 biyo bayan ganin jinjirin watan da aka yi da yammacin Lahadi. Da wannan ake sa ran al'ummar musulmin ƙasar su tashi da azumi a ƙasa kamar yadda jaridar Arab News ta rawaito.
Read More
‘Yan daba sun yi wa filin jirgin saman Haiti dirar mikiya

‘Yan daba sun yi wa filin jirgin saman Haiti dirar mikiya

Kwana guda bayan da gungun ‘yan daba suka ɓalle manyan gidajen yari biyu a Haiti, a yau kuma sun farwa babban filin jirgin saman ƙasar da nufin karve iko da shi. Wannan ta sa dole ƙasashen da ke maƙwaftaka da Haiti suka fara ƙarfafa tsaron kan iyakokin su don gudun fantsamar ‘yan dabar zuwa cikin su. Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda aka riƙa musayar wuta tsakanin jami’an sojoji da kuma ‘yan dabar sama da 500. Har kawo yanzu filin jirgin saman na The Toussaint Louverture na kulle yayin da aka dakatar da duk wata zirga-zirga. Ko a makon da ya…
Read More
Ghana na bikin cika shekara 67 da samu ‘yancin kai

Ghana na bikin cika shekara 67 da samu ‘yancin kai

Daga BASHIR ISAH A wannan Larabar ƙasar Ghana ke bikin cika shekara 67 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Ghana ta shafe shekara 83 a ƙarƙashin Turawan mulkin mallaka kafin daga bisani ta samu 'yancin kanta. Shugaban ƙasar na farko, Dr Kwame Nkrumah, ya bayyana samun 'yancin ƙasar a matsayin babban cigaba gane da shugabancin ƙasar. Ranar 6 ga Maris ta kowace shekara Ghana ke bikin ranar zagayowar samun 'yancin kai. Bikin wannan karon zai gudana ne a dandalin Youth Resource Centre da ke Koforidua. A 2017 ne Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya ɗauki matakin jujjuya in…
Read More
Afrika ta yi tir da hare-haren Isra’ila a Gaza

Afrika ta yi tir da hare-haren Isra’ila a Gaza

*Falasɗinu ta yi maraba da taron AU Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugabannin ƙasashen Africa sun yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke ƙaddamarwa kan yankin Gaza da sunan kare kai, yayin da suka buƙaci ƙasar ta dakatar da varin wutar  ba tare da vata lokaci ba. Moussa Faki Mahamat, shugaban majalisar gudanarwar ƙungiyar ta AU ya ce wannan luguden wuta, babu abinda ke cikinsa illa cin zali da cin zarafi, kuma lokaci ya yi da duniya za ta mayar da Isra’ila cikin hayyacin ta. Kalaman na Faki na zuwa ne bayan doguwar maƙala da Prime ministan Falasɗinu…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Ghazouani ya zama sabon Shugaban AU

Da Ɗumi-ɗumi: Ghazouani ya zama sabon Shugaban AU

Daga BASHIR ISAH Shugabannin ƙasashen Afirka ƙarƙashin Ƙungiyar Haɗi Kan Afirka (AU) sun zaɓi Shugaban Ƙasar Mauritania, Mohamed Ould Ghazouani, a matsayin sabon shugaban AU na 2024. Ghazouani ya gaji wannan kujera ne daga Shugaba Azali Assoumani na ƙasar Comoros, wanda ya yi riƙe shugabancin ƙungiyar a 2023. ’Yan Majalisa Wakilai 60 sun buƙaci a sauya fasalin Nijeriya Bankin Access ya naɗa sabuwar Babbar jamiar zartarwar rukunin bankunan ta riƙon ƙwarya An yi zaɓen a ranar Asabar, 17 ga Fabrairu yayin babban taron ƙungiyar karo na 37 wanda ke gudana a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
Read More
Shugaban Ƙasar Namibiya ya rasu yana da shekara 82 a duniya

Shugaban Ƙasar Namibiya ya rasu yana da shekara 82 a duniya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasar Namibiya, Hage Geingob, ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, kamar yadda ofishinsa ya bayyana. Marigayin ya rasu ne sakamakon fama da cutar daji. Geingob ya mutu ne a ranar Lahadi a asibitin Lady Pohamba da ke Windhoek, babban birnin kasar, inda da matarsa ​​da 'ya'yansa suka kasance a gefensa, in ji Mukaddashin Shugaban Kasar, Nangolo Mbumba, a wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na Geingob. Mbumba ya ce "Al'ummar Namibiya ta yi rashin wani fitaccen hadimin jama'a, mai fafutukar kwato 'yanci, babban mai tsara tsarin mulkinmu da kuma ginshikin Namibia," in…
Read More
Ukraine na zargin wasu jami’anta da wawushe mata kuɗin makamai

Ukraine na zargin wasu jami’anta da wawushe mata kuɗin makamai

Daga BASHIR ISAH Binciken gwamnatin Ukraine ya bankado cewar wasu jami’an hukumar kula da makaman kasar sun hada baki da takwarorinsu na ma’aikatar tsaro, wajen karkatar da kusan Dala miliyan 40, da aka ware domin sayen makamai. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke tsaka da fafata yaki tsakaninta da Rasha. Ya zuwa yanzu an gurfanar da mutum biyar a kotu kan zargin yin rub-da-ciki a kan kudin maka kamar yadda masu gabatar da kara suka bayyana. Kazalika, bayanan gwamnatin Ukraine sun ce ana tsare da wani guda da aka cafke shi a lokacin da yake kokarin…
Read More