19
Jul
Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a filinku na Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan makon za mu yi magana ne game da auri-saki a ƙasar Hausa. Ko ba a gaya maka ba mai karatu za ka yi wa kanka alƙalanci cewa ƙasar Hausa tana neman zama shalkwatar mace-macen aure a Nijeriya. Domin idan ka dubi sauran ƙabilu, ba su fiye samun wannan matsala ta saurin mutuwar aure da sakewa ba kamar yadda muke yi a nan yankin. A 'yan kwanakin nan ma da aka yi ta zance game da…