Ra’ayi

Akwai buƙatar malamai su duba lamarin walimar sauka da ake yi yanzu

Akwai buƙatar malamai su duba lamarin walimar sauka da ake yi yanzu

Daga SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI, Zariya A zamanin dauri duk lokacin da iyaye suka ga 'ya'yansu sun kusa sauke Alkur'ani mai girma zuciyarsu kan cika da murna da farin ciki ne tare da fatan Ubangiji ya nuna musu lokacin. Idan ranar ta taho masu aka tabbatar da hakan, iyaye kan bi malamai da kyautar da ba ta taka kara ta karya ba don nuna godiya ga malaman da kara musu kwarin gwiwa domin su kara jajircewa kan abinda suke yi, su kuma su karva suna farin ciki da matukar godiyar karamcin da iyayen yara suka nuna musu. Idan makarantar allo ce,…
Read More
Fargabar matsalar tattalin arzikin Nijeriya

Fargabar matsalar tattalin arzikin Nijeriya

A makon da ya gabata, Bankin Duniya ya fitar da rahotonsa kan tabarberewar tattalin arzikin Nijeriya. Rahoto a karkashin duba irin cigaban da Nijeriya ta samu, Cibiyar Hada-hadar Kudi Ta Duniya ta bayyana cewa, tabarbarewar yanayin tattalin arzikin Nijeriya na kara jefa al'ummar kasar cikin wani hali. Rahoton ya nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki ya zama annoba ga rayuwar ’yan Nijeriya wanda dole ne hukumomi su yi yaki da hakan. Habakar hauhawar farashin kayayyaki da ke fitowa daga matsalar rashin tsaro, Bankin ya ce, zai iya jefa karin 'yan Nijeriya miliyan daya cikin matsanancin talauci. Tabbas tashe-tashen hankulan da hauhawar…
Read More
Fitar matasan Arewa ƙasashen waje: Ya kai mai shirin fecewa, ga wata ’yar shawara

Fitar matasan Arewa ƙasashen waje: Ya kai mai shirin fecewa, ga wata ’yar shawara

Daga MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI A mafi yawan lamura, za ka samu akwai alheri, kuma akan samu akasinsa. Don haka, a irin wannan dambarwar da mafi girman abin da ya jawo ta shi ne rashin kyakkyawan shugabanci, dole sai an yi taka-tsan-tsan. Lallai masu jan ragamar jagorancin al'umma a Najeriya, yawancinsu suna ha'intar al'umma.  Wani bawan Allah yake cewa da fita ko fecewa daga qasa abu ke mai sauki, to watakila shugabannin kasarmu sai dai su juyo su ga ba kowa, kowa ya kama gabansa. To shi dan'adam da Allah ya yi shi ba ya son a hana shi walwalar abin…
Read More
Tasirin fina-finan Hausa sun wuce yadda ake ɗaukar su a ƙasar Hausa

Tasirin fina-finan Hausa sun wuce yadda ake ɗaukar su a ƙasar Hausa

Daga ZAHRADDEEN IBRAHIM KALLAH Wato fina-finan Hausa sun yi nisa wajen jan hankalin al'umma. Ko shakka babu wannan dama ce da za a yi amfani da ita wajen sauya tunanin al'umma zuwa ingantatciyar rayuwa da bin dokoki.  Kwanakin baya a kafofin sada zumunci har majalusu na unguwanni, maganar da na ji ana ta yi ita ce wai raba gardama ya bayyana. Da yake na kwana biyu ba na kallo, na ce wanene wannan raba gardama? Ashe a cikin shirin Labarina ne na Malam Aminu Saira. A satin nan da muka fita daga shi, sai na ji sabon batu. Ko'ina maganar…
Read More
Basaja a zaman aure (1)

Basaja a zaman aure (1)

Tare da AMINA YUSUF ALI Sannunku da jimirin karatun shafin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja! A wannan mako mun kawo muku yadda wasu ma'aurata suke yin basaja a zaman aure. Wanda abu ne da yake taka muhimmiyar rawa wajen kawo rikici a gidajen aure har ma idan abu ya yi kamari ya kai ga rusa auren gabadaya. To wai meye basaja? Na san mai karatu zai so ya san ma'anar basaja. Basaja kamar sani azancin maganar nan ne da ake cewa kitsen rogo. Wannan azancin na nufin kamar yadda muka sani rogo yana da fari, musamman danyensa…
Read More
Shin a Nijeriya ma ana yin digirin siyarwa?

Shin a Nijeriya ma ana yin digirin siyarwa?

Daga MUSA AYUBA IBRAHIM Akwai wani da ya nuna min wani babban ma'aikacin gwamnati ya ce: su na shekararsu ta karshe suka fara ganin sa, yana shigowa jifa-Jifa lakca ya zo su gaisa, bayan gama jami'ar sai ga sunan sa a jerin waɗanda suka kammala digiri. Ba su san shi ba tun daga farko sai shekarar karshe a zango karshe. Wani dan uwa na an tava masa tallan Irin wannna digirin a wata jami'a a kan wani i adadin kudi amma na bashi shawarar hakura gaskiya duk da har samfuri sun nuna masa da misalan mutanen da aka musu. Saboda…
Read More
Mu mayar da hankali ga yin gwaji kafin aure

Mu mayar da hankali ga yin gwaji kafin aure

Tare da ABBA ABUNAKAR YAKUBU Zainab wata matashiya ce da ke koyon aikin jinya, kuma take daf da daidaita zancen aure tsakaninta da wanda take so ta aura. Sanin muhimmancin yin gwajin kwayoyin halittar jini ga aurenta, ya sa ta garzaya domin duba nau'in kwayar halittar jininta a wani asibiti da ke cikin garin Katsina. Sai dai ga mamakinta sakamakon da ya fito ya tsoratata ganin cewa tana dauke ne da nau'in genotype mai AS, savanin abin da take sa rai ta gani na AA, wanda a cewarta akasari 'yan gidansu ke da shi. Babu shakka wannan sakamako ya girgiza…
Read More
Badaƙala da haƙƙoƙin talakawa, ya isa haka!

Badaƙala da haƙƙoƙin talakawa, ya isa haka!

Tate da ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ƙarshe dai tsohuwar Ministar Ma’aikatar Jinkai da Yaki da Talauci Betta Edu ta yi gaba, sai dai tashin zance. Amma ’yan Nijeriya za su dade ba su manta da ita ba a matsayinta na minista mai gajeren kwana, wacce cikin kankanin lokaci son zuciya da rashin gaskiya suka yi awun gaba da kujerarta. Dama a cikin jawabinsa na sabuwar shekara, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa da ’yan Nijeriya cewa kamar yadda ya dauki rantsuwar kama aiki na yin dukkan abin da ya kamata don inganta cigaban kasar nan. Shi da ministocinsa da…
Read More
Cin zarafi a aure: Ina mafita (2)?

Cin zarafi a aure: Ina mafita (2)?

Tare da AMINA YUSUF ALI Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Blueprint manhaja. Yau ma ga mu a wani makon mai albarka. A wannan makon muna tafe ne da bayani a kan yadda matan auren da suke fuskantar cin zarafi a gidan aure musamman a kasar Hausa. Inda za ka ga cewa, mace ana cin zarafinta, ana hana ta abinci, da sauran hakkokinta na aure ga uwa uba kuma duka da wulakanci. Amma ta kafe ta haqura ta zauna a gidan. Me yake kawo hakan? Kuma meye mafita? Yawanci sukan dauki matakin hadiye komai su cigaba da…
Read More
Edu ba ta cinye Baitulmali du ba

Edu ba ta cinye Baitulmali du ba

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Batun almundahana a Nijeriya ai ba sabon abu ba ne don kama daga lokacin mulkin soja har dawowa farar hula da a ke ciki yanzu daga 1999, kalubalen ya zama ruwan dare a Nijeriya. A baya an dau abun ba wani babba ba ne da ya wuce wasu baragurbi a jami'an 'yan sanda da kan karbi kudi 'yan kalilan daga direbobi a kan tituna don kyale su su wuce ba tare da wani bincike ba. Hakanan in mutum na son a bar shi ya ketare wani shinge da ba shi da hurumi sai ya riqe…
Read More