Siyasa

Zaɓen 2023: Aski ya zo gaban goshi!

Zaɓen 2023: Aski ya zo gaban goshi!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Azancin zancen Hausawa na cewa aski in ya zo gaban goshi ya fi zafi duk da ba lalle kowa ya kan ji zafi don askin da a ke yi ma sa ya zo goshi ba. Gaskiya ma hakan ya danganta ga wanzamin da ya ke askin. Idan an samu goni ya jika sabulu da ɗan ruwa mai sanya ya shafa ya murza aska sai askin ya yi sanyi kuma har ma a riƙa hira tsakanin wanzamin da wanda a ke yi wa askin. Shin wannan zaɓen ya na zafi ko ba shi da shi a zahiri…
Read More
Gangamin APC ya gamu da cikas a Yobe

Gangamin APC ya gamu da cikas a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu Ɗaruruwan 'yan dabar siyasa sun haifar da cikas a gangamin yaƙin neman zaɓen Jam'iyyar APC na shiyya ta uku (Zome C). Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a garin Gashuwa, shalkwatar Ƙaramar Hukumar Bade da ke jihar Yobe, mahaifar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya. An tsara aiwatar da gangamin ne bayan buɗe sabuwar kasuwar zamani wadda Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, ya gina a garin Nguru inda daga bisani aka hallara a Filin Agric da ke unguwar Katuzu a Gashuwa. Bugu da ƙari, tun a garin Nguru aka fara ganin alamun yi wa tawagar…
Read More
Dalilin fuskantar ƙarancin sabbin takardun Naira – Emefiele

Dalilin fuskantar ƙarancin sabbin takardun Naira – Emefiele

Daga WAKILINMU Babban Bakin Nijeriya ta bakin shugabansa, Godwin Emefiele, ya bayyana dalilin da ya haifar musu da tsaiko wajen samar da sabbin takardun Naira da aka sauya wa fasali a wadace. A Emefiele, a halin yanzu Babban Bankin ba shi da halin buga sabbin takardun kudin da za su wadata kasar saboda takardun da ake buga kudin da su sun yanke. Ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a yayin da yake yi wa Majalisar Ƙasa jawabi kan batun sauya fasalin takardun Naira. Majiyar Jaridar Premium Times da ta halarci zaman Majalisar ta ruwaito cewa, Emefiele ya koka kan…
Read More
Sanata Bwacha ya zama ɗan takarar Gwamna na APC a Taraba

Sanata Bwacha ya zama ɗan takarar Gwamna na APC a Taraba

Daga WAKILINMU Sanata Emmanuel Bwacha ya lashe zaɓen fidda gwani na Jam'iyyar (APC) da aka maimaita a matsayin ɗan takarar gwamna na Jihar Taraba . Wannan na zuwa ne yayin da zaɓen gwamnoni ya ƙarato, wanda za a gudanar 11 ga Maris. A zaɓen da aka sake, Bwacha ya samu ƙuri'u 778 yayin da abokin hamayyarsa, Yusuf Yusuf ya damu biyar. Baki ɗaya, dalaget 796 aka tantance yayin zaɓen.
Read More
Kada ka ɓata dangantaka saboda siyasa – Nasihar Sarkin Musulmi ga Atiku

Kada ka ɓata dangantaka saboda siyasa – Nasihar Sarkin Musulmi ga Atiku

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da ake tsaka da zazzzafan yaƙin neman zaɓe don tunkarar kakar zaɓe mai zuwa ta 25 ga Fabrairu, Sarkin Musulmi na Sokoto, Mai alfarma  Sa’ad Abubakar (III), ya gargaɗi 'yan siyasa a kan su kauce wa siyasar zagi da cin mutuncin juna.  Sultan ɗin ya yi wannan kira ne a ranar Talatar da ta gabata a lokacin amsar baquncin ɗan takarar shugaban ƙasar nan a qarqashin jamiyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya kawo masa ziyara a yayin shirin fara gangamin yaqin neman zabensa a jihar.  A cewar Sarkin Musulmi: "Duk abinda mutum zai yi,…
Read More
Gwamna Bala ya yi wa jama’ar Dambam alƙawarin masarauta idan suka sake ba shi damar wa’adi na biyu

Gwamna Bala ya yi wa jama’ar Dambam alƙawarin masarauta idan suka sake ba shi damar wa’adi na biyu

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammad ya bai wa al'ummar Dambam tabbacin masarauta matuqar suka sake ba shi damar mulki wa'adi na biyu a wannan zaɓe dake tafe. “Idan ɗaukacin ku, kuka jefa min mafi yawan ƙuri’o’inku waɗanda a fayyace za su zarta mafi yawan ƙuri’o’i da zan samu a ƙaramar hukumata ta Alkaleri a zaɓen ranar 11 ga watan Maris, kuna da tabbacin cewa zan ƙirƙiro maku masarautar sarki mai daraja ta biyu a garin Dambam,” Gwamna ya shaidar masu. Gwamna Bala Mohammed ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da tawagar yaqin neman…
Read More
Tinubu bai cancanci shugabancin Nijeriya ba, inji Abubakar Billy, jikan Tafawa Ɓalewa

Tinubu bai cancanci shugabancin Nijeriya ba, inji Abubakar Billy, jikan Tafawa Ɓalewa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi A kwanakin baya ne dai, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, a cikin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Chanels, ya yi tsokaci da cewar, akwai wasu jami’ai dake cikin Fadar Shugaban Ƙasa waɗanda ba su so Tinubu ya kasance ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC ba. Ya ce waɗannan mutane suna yin bultu don ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi abinda ya dace. El-Rufa’i ya ce, “akwai wasu gungu a fadar shugaban ƙasa da suke yin da’awar mu faɗi zaɓe."  Wakilin Blueprint Manhaja na daga cikin wasu manema labarai da…
Read More
BIDIYO: Za mu ci gaba da amfani da tsohuwar Naira a Kaduna nan da shekara 4 – El-Rufai

BIDIYO: Za mu ci gaba da amfani da tsohuwar Naira a Kaduna nan da shekara 4 – El-Rufai

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ba za a daina karɓar tsohuwar Naira, N200, N500 da N1000 ba a jihar har zuwa shekaru huɗu masu zuwa. Ya faɗi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta na zamani a ranar Laraba. "Ina muku alƙawari, duk ɗan jihar Kaduna da ke da tsohon kudi ya ci gaba da amfani da shi, za mu amsa daga nan har shekara huɗu," in ji shi. Kalli bidiyon don ƙarin bayani:
Read More
Nasarawa 2023: Zan bai wa masarautun gargajiya fifiko – Yakubu Maidoya

Nasarawa 2023: Zan bai wa masarautun gargajiya fifiko – Yakubu Maidoya

Daga JOHN D. WADA, A LAFIYA Ɗan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a Jam’iyyar NNPP, Alhaji Abdullahi Yakubu Maidoya, ya ce idan al’ummar jihar suka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar a zaɓen gwamnan jihar da ke tafe zai tabbatar ya inganta tare da ɗaukaka harkokin masarautun gargajiyar jihar baki ɗaya ta yadda za su yi daidai da zamani ba kamar yadda lamarin yake a yanzu ba. Yakubu Maidoya ya bayyana haka ne a ci gaba da kamfen ɗinsa da yake yi a lokacin da ya ziyarci masarautar Keana, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keana da ke jihar. Da yake bayyana wa Sarkin…
Read More
2023: Maidoya ya gana da shugabannin NNPP na ƙananan hukumomi a Nasarawa

2023: Maidoya ya gana da shugabannin NNPP na ƙananan hukumomi a Nasarawa

*Ya buƙace su su riƙe amana Daga JOHN D. WADA, a LAFIYA Don tabbatar da nasarar jam’iyyar NNPP a duka matakai a jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya, ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar NNPP, Abdullahi Yakubu Maidoya, ya yi wani zama na musamman da duka shugabannin jam’iyyar na duka ƙananan hukumomi 13 da na gundumomin jihar. Zaman wanda aka yi a babban sakatariyar jam’iyyar dake garin Lafiya, babban birnin jihar, ya samu goyon bayan duka shugabannin ya kuma samu halarcin wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar daga ciki da wajen jihar. Da yake jawabi, Yakubu Maidoya ya gode…
Read More