Siyasa

2023: Mun gamsu da manufofi biyar na Atiku, inji Uwani Hamsal

2023: Mun gamsu da manufofi biyar na Atiku, inji Uwani Hamsal

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Wata 'yar siyasa a Jihar Gombe kuma jigo a tafiyar yaqin neman zaven ɗan takarar gwamnan jihar a Jam'iyyar PDP Muhammad Jibrin Barde, Hajiya Uwani Hamsal, ta ce 'yan Nijeriya sun gamsu da ajandoji 5 da ɗan takarar shugabancin Nijeriya Atiku Abubakar, ya zayyana. Hajiya Uwani Hamsal, ta ce ajandoji 5 da suka ƙunshi, inganta tsaro da farfaɗo da harkar noma, da ilimi da kasuwancin da kuma samar da ayyukan yi ga 'yan Nijeriya da ma su ne abinda suka daɗe suna ci wa 'yan Nijeriya tuwo a ƙwarya. Hajiya Uwani, ta bayyana hakan…
Read More
Idan na ci zaɓe zan kammala aikin haƙar man Kolmani —Tinubu

Idan na ci zaɓe zan kammala aikin haƙar man Kolmani —Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takaran Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, ya ce idan ya ci zave zai tabbatar aikin haƙo man fetur na garin Kolmani da ke Jihar Gombe bai tsaya ba. Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin yaƙin neman zaɓensa a Jihar Gombe, inda ya ce muddin aka zaɓe shi gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen kammala aikin. “Zan tabbatar gwamnatina ta ɗora kyawawan ayyuka daga inda Shugaba Muhammad Buhari ya tsaya,” inji Tinubu. Tinubu, ya kuma yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na gina gandun masana’antu a…
Read More
Na cika alƙawuran da na ɗauka wa ‘yan Nijeriya – Buhari

Na cika alƙawuran da na ɗauka wa ‘yan Nijeriya – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa alƙawuran yaƙin neman zaɓen 2015 da ya yi wa ‘yan Nijeriya gwamnatinsa ta cika. Shugaban ya bayyana haka ne a wajen bikin yaye ɗaliban Jami’ar Tarayya karo na 7 da aka yi a garin Oye-Ekiti na Jihar Ekiti, inda ya bayyana cewa ya bayar da gudunmawa ta fuskar tattalin arziki, tsaro, da yaƙi da cin hanci da rashawa. Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙungiyar Benchers ta Nijeriya Cif Wole Olanipekun (SAN) da tsohon manajan darakta na bankin First Bank Bisi Onasanya da kuma tsohon kyaftin ɗin Super…
Read More
Jirgin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima ya sauka Borno

Jirgin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima ya sauka Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Maiduguri Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima da wasu gwamnoni biyar sun yi wa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno tsinke domin gudanar da yaƙin neman zaɓe. Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, da takwarorinsa na jihohin Yobe da Gombe, haɗi da jiga-jigan gwamnatin Jihar Borno, su ne tarbi tawagar ɗan takarar da ƙusoshin Jam'iyyar APC yayin gangin da ya gudana ran Asabar. Jim kaɗan da saukarsa a Maiduguri, Tinubu da jiga-jigan jam'iyyar APC suka shiga tattaunawa ta musamman da masu ruwa da tsaki a babban ɗakin taro…
Read More
Ƙarancin Naira da man fetur barazana ce ga takarar Tinubu – Gbajabiamila

Ƙarancin Naira da man fetur barazana ce ga takarar Tinubu – Gbajabiamila

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya danganta matsalar da ake fuskanta a halin yanzu na ƙarancin man fetur da ƙarancin Naira ka iya daƙile nasarar ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu na cin zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu. Gbajabiamila ya bayyana haka ne a Legas ranar Talata a lokacin ƙaddamar da shirin raba motocin sufuri mai taken: ‘Gbaja Ride’ ga mazaɓarsa ta Surulere. Motocin bas guda 35 masu saukin farashi za su riƙa bin hanyoyi daban-daban a Surulere da kewaye. “A matsayina na wakilinku kuma mai magana da yawunku, Ina…
Read More
APC ta dakatar da ‘yar takarar gwamnanta a Adamawa

APC ta dakatar da ‘yar takarar gwamnanta a Adamawa

Daga BASHIR ISAH Shugabancin Jam'iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu a Jihar Adamawa ta dakatar da mai yi wa jam'iyyar takarar gwamna a jihar, Sanata Aishatu Ahmed Dahiru Modibbo (Binani), daga jam'iyyar. Wasiƙar dakatarwar wadda ta samu sa hannun jami'an jam'iyyar 21, ta nuna an ɗauki matakin dakatar da Binani na tsawon wata shida daga jam'iyyar ne saboda zargin rashin biyayya ga kotu da ake yi mata. Kazalika, shugabannin jam'iyyar sun zargi Binani da haddasa ɓangaranci da rarraban kan mambobin jam'iyyar. Wannan na zuwa ne yayin da ya rage 'yan kwanaki kafin zaɓen gwamnoni a faɗin ƙasa. Ga…
Read More
Gangamin zaɓen 2023: APC ta bayyana gamsuwarta da goyon bayan al’ummar Jihar Yobe

Gangamin zaɓen 2023: APC ta bayyana gamsuwarta da goyon bayan al’ummar Jihar Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Yobe, Alhaji Muhammed Gadaka ya nemi haɗin kan dukkan magoya bayan Jam'iyyar APC a Yobe ta Kudu domin samun nasarar babban zaɓe mai zuwa na 2023. Shugaban Jam’iyyar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a yaƙin neman zaɓen da Jam’iyyar APC ta gudanar a shiyya ta biyu (Zone B), a filin wasa na Dabo Aliyu da ke ƙaramar hukumar Potiskum a Jihar Yobe. Gadaka ya bayyana cewa, sai ta hanyar cikakken haɗin kai da goyon bayan al’ummar yankin ne Jam’iyyar APC za ta samu nasarar lashe…
Read More
Har yanzu CBN bai sakar wa INEC kuɗaɗe ba – Kwamishina

Har yanzu CBN bai sakar wa INEC kuɗaɗe ba – Kwamishina

Daga BASHIR ISAH Yayin da ya rage kwanaki kaɗan kafin zaɓen 2023, har yanzu Babban Bankin Nijeriya (CBN) bai sakar wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), kuɗaɗen da take buƙata domin tura kayayyakin zaɓe zuwa sassan ƙasa ba. A makon jiya Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya gana da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, inda suka tattauna yiwuwar bai INEC sabbin kuɗin da za ta yi amfani da shi wajen tura kayan zaɓe zuwa sassa. Inda a nan Emefiele ya bai wa INEC tabbacin ba zai bari a yi wa CBN kallon ana amfani da shi wajen yi wa…
Read More
Jerin mazaɓu 240 da INEC ta ce ba za a gudanar da zaɓe a cikinsu ba

Jerin mazaɓu 240 da INEC ta ce ba za a gudanar da zaɓe a cikinsu ba

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta fitar da jerin sunayen mazaɓun da ta ce zaɓe ba zai gudana a cikinsu ba saboda rashin rijistar masu kaɗa ƙuri'a. Tun da fari, Shugaban INEC na Ƙasa, Mahmood Yakubu, ya bayyana a ranar Litinin cewa mazaɓun da lamarin ya shafa ba su da mutum ko guda da aka yi wa rijistar zaɓe a ƙarƙashinsu. A cewarsa, baki ɗaya mazaɓu 176,606 ake da su a faɗin ƙasa. Ya ƙara da cewa, waɗanda aka sauya wa mazaɓa za su samu saƙon tes ta waya mai ɗauke da bayanin mazaɓar da aka tura mutum…
Read More
Dalilin soke taron Atiku a Ribas – PDP

Dalilin soke taron Atiku a Ribas – PDP

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP a Jihar Ribas, ya ce an soke gangamin kamfe na Atiku Abubakar da aka shirya gudanarwa a Fatakwal don kauce wa asarar rayuka. Shugaban Kwamitin a Jihar Ribas, Sanata Lee Maeba ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya shirya ranar Litinin a Fatakwal, babban birnin jihar. Maeba ya ce an kai wa mambobin PDP da magoya bayan Atiku hare-hare a tsakanin watanni ukun da suka gabata a jihar. Kazalika, ya yi zargin Gwamnatin Ribas ta rufe harkokin kasuwancin wasu jiga-jigan mambobin jam’iyyar masu mara…
Read More